✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar Attahiru: An kafa kwamitin binciken haduran jiragen saman soji

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, NAF, ta ce ta kafa wani kwamiti da zai binciki haduran jiragen samanta. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin…

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, NAF, ta ce ta kafa wani kwamiti da zai binciki haduran jiragen samanta.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke bayyana damuwarsu biyo bayan hadarin jirgin sama har sau uku da ya faru a cikin wata uku; da suka lakume rayukan jami’an tsaron akalla 18.

Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata, ya bayyana cewa kwamitin da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao ya kafa ya kunshi manyan jami’an tsaron da ke aiki tare da takwarorinsu da suka yi ritaya.

Ya ce mambobin kwamitin za su gudanar da binciken lafiyar dukkanin jiragen rundunar wadanda suke aiki, sannan Babban Hafsan ya umarci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa nan da 18 ga Yuni 2021.

A cewarsa, Mataimakin Kwamandan Operation HADIN KAI, Air Vice Marshal Abraham Adole ne zai jagoranci kwamitin.

“Kwamitin zai yi binciken bayanan lafiyar jiragen sashen ayyuka da gyaran jiragen sannan ya nazarci lafiyarsu a halin yanzu daga bisani ya bayar da shawarwarin matakan yadda za a inganta lafiyar jiragen.

“Kwamitin zai kuma yi aiki tare da kwararrun injiniyoyi da masana harkar jiragen domin jin shawarwari da gudumawa daga gare su kan yadda za a inganta lafiyar jirage,’’ a cewar sanarwar.

A makon jiya ne, Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru, ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna tare da wasu manya da kananan hafsoshin sojin kasar.