✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar Bantex babban rashi ne a Kudancin Kaduna — APC

Shugaban jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Ibrahim Koli ya bayyana mutuwar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex, a matsayin babban rashi…

Shugaban jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Ibrahim Koli ya bayyana mutuwar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex, a matsayin babban rashi ga Kudancin Kaduna.

Alhaji Koli ya ce za a dade ana tunawa da Bantex saboda fadin gaskiya ga kowa ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da wakilin Aminiya kan mutuwar tsohon mataimakin gwamnan a ranar Lahadi.

A cewarsa, “Wasu da dama ba sa kaunar sa ne saboda ba ya goyon bayan kabilanci ko wariyar addini ga wasu bangare na mutanen Kudancin Kaduna da wasu ke kallo a matsayin baki.

“Ya kasance ya fuskanci gagarumar gaba daga jama’ar da ba sa son gaskiya a yankin, amma yanzu za su gane amfaninsa bayan baya nan.” Inji shi

Barnabas Bala mai shekaru 64 a duniya, ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja a ranar Lahadi, bayan wata doguwar jinya ta rashin lafiyar da ya dade yana fama da ita.

A cikin takardar sanarwar da ta fito daga gwamnatin Jihar Kaduna mai dauke da sa hannun Gwamna Malam Nasir El-Rufai, ta bayyana Barnabas Bala a matsayin mutum mai hangen nesa kuma abin dogaro da ya hidimta wa jama’ar Karamar Hukumar Kaura da na Jihar Kaduna a mataki daban-daban.

Bantex ya kasance Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, a wa’adin mulkin Gwamna El-Rufai na farko.

A shekarar 2019 ce ya ki neman tazarce tare da Gwamna El-Rufai, domin neman kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Kaduna ta Kudu.

Rashin neman tazarcen ya bar magoya bayansa da sauran jamaa cike da mamaki da taraddudin ko zai kai bantensa kuwa.

Sai dai bayan zabamma ya sha kasa a hannun Sanata Danjuma La’ah, abinda ake ganin tasirin jam’iyyar PDP a Kudancin Kaduna da kuma irin takun sakar da ya rika gudana na bambancin siyasa tsakanin mafiya rinjayen jama’ar Kudancin Kaduna.

Marigayi Bantex ya taba zama Shugaban Karamar Hukumar Kaura kafin daga baya ya zama dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Kaura.