✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

N-Power: An fara biyan matasan da aka rike kudadensu

Za a biya matasa 9,066 N150,000 kowannensu

An fara biyan matasan da suka yi aikin N-Power a shekarun 2016 da 2018 kudadensu da Gwamnatin Tarayya ta rike.

Ma’aikatar kula da ayyukan jinkai da kyautata rayuwa ce ta sanar da biyan matasan.

A shekarar 2020 ne ma’aikatar ta dakatar da biyan albashin mutum 14,021 daga cikin matasan saboda dalilai daban-daban, ciki har da wadanda aka gano suna karbar albashi a ma’aikatu da hukumomin gwamnati, sabanin ka’idar aikin na N-Power, wanda aka samar domin matasa marasa aiki.

Babban Sakataren Ma’aikatar, Bashir Nura Alkali, ya shaida mana cewa “bayan gudanar da cikakken bincike” an tantance 9,066 daga cikin matasan domin biyan su “kuma kowannensu za a biya shi N150,000.

“Sauran 4,955 kuma an rike kudadensu zuwa lokacin da za a kammala bincike. Duk wanda aka samu da laifi kuma za a hukunta shi daidai da laifinsa”, inji shi.