✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na bai wa lauya N2m ya kai wa alkali don a sake ni —Abduljabbar

Malamanin ya nemi a dawo masa kudin da ya bai wa lauyan bayan alkali bai sake shi ba.

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ake zargi da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a karatuttukansa, ya zargi lauyansa da karbar Naira miliyan biyu daga hannunsa, don bai wa alkali a sake shi.

Ya tsegunta cewa lauyan nasa, Barista Dalhatu Shehu Usman, ya karbi kudin a hannunsa ne a lokacin da kotun take karbar yankan hanzarin bangarensa da na masu kara, a wani bangare na kawo karshen shari’ar.

Ya shaida wa kotun cewa, “A wani lokaci lauyana, Dalhatu ya zo ya same ni ya gaya min cewa alkali ya gaya masa cewa idan ba don mutum biyu ba, to da zai sake ni, wato saboda dan uwana Karibu da kuma Alkalin Alkalai.

“A nan yake gaya min cewa amma idan har zan yi kokari na ba shi (alkalin) Naira miliyan biyu, to zai sake ni.

“Bayan na bayar da kudin ne kuma na ga ba a sake ni ba kamar yadda ya yi min alkawari, sai na nemi a dawo min da kudina, amma sai ya ba ni hakuri cewa na jira har zuwa irin wannan rana,” in ji malamin.

Abduljabbar Kabara, ya shaida wa Mai sharia Ibrahim Sarki Yola cewa, wajibi ya tona asiri, tun da ba a yi amfani da kudin da ya bayar a matsayin fansarsa ba.

‘Ba zan taba bayar da cin hanci ba’

A cewarsa, yana gudun kudin za su iya zama cin hanci, wanda shi ba zai taba amincewa ya bayar ba.

“Ni dama na bayar da kudin ne a matsayin fansar kaina, amma ba zan taba bayar da cin hanci ba domin da na bayar da cin hanci gara a rataye ni,” in ji shi.

Ya shaida wa kotun cewa Barista Dalhatu Shehu Usman ya shaida masa cewa ya raba kudin ne inda ya bai wa alkali Naira miliyan daya da dubu dari uku sai kuma dubu dari biyu da aka ba wani babban mutum, yayin da ya sanya Naira dubu dari biyar a aljihunsa.

Sai dai alkalin kotun ya musanta karbar wannan kudi da wanda ake kara ke da’awar ya bayar don a ba shi, inda ya jaddada cewa tun daga lokacin da ya umarci Barista Dalhatu da ya zama lauyan Abduljabbar din, bai sake yin magana da shi ba.

Kazafi Abduljabbar ya yi min —Lauyansa

Da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, Lauyan da yake kare Abduljabbar din ya musanta batun karbar kudi daga hannun malamin.

“Wannan magana karya ce; Ni ban yi mamaki ba domin wannan halinsa ne.

“Idan an duba, ya yi makamancin irin wannan zargi a kan lauyoyinsa kafin ni. a cikinsu ma akwai wadanda ya zarga da neman matarsa.”

Matsalar da muka samu da Abdulabbar —Barista Dalhatu

A cewar Barista Dalhatu, sun sami matsala da wanda yake karewa ne tun bayan da kotun Abuja ta ci tarar su Naira miliyan 10, inda ya yi zargin hadin baki ne.

“Mun sami matsala ne bayan da kotun Abuja ta yanke hukuncin biyan tarar Naira miliyan 10 inda ya yi zargin wai ni na hada baki da kotun don na karbi wannan kudi daga wurinsa.”

Ya kuma barranta kansa da ci gaba da kare malamin a sauran shari’ar da ke gaban kotuna daban-daban.

“Ni yanzu ba lauyansa ba ne domin na je kotunan da muke da kes a gabansu duk na zare hannuna a matsayin lauyansa. Haka ya sa ko a yau ban halarci zaman kotun ba sai na turo wakili,” in ji shi.

Barista Dalhatu ya ce ba zai dauki matakin shari’a a kan malamin ba sai dai “zan nemi hukumomi su gudanar da bincike a kan wannan zargi domin a wanke ni a idon duniya.”

Kotu ta karba bayanan bangarorin da ke shari’ar

Tunda farko bangarorin masu gabatar da kara da kuma na wanda ake kara sun gabatar wa kotu bayanansu na karshe a rubuce.

Lauyan masu gabatar da kara, Farfesa Mamman Lawan Yusufari (SAN) ya nemi kotun da ta karbi bayanansu a matsayin hujjojin da za ta yi la’akari da su wajen yanke wa wanda ake zargi hukuncin da ya dace da laifin da ake tuhumar sa na yin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

A nasa bangaren, wanda ake kara Abduljabbar Kabara, ya nemi kotun da ta yi la’akari da kaset din karatuttukansa da ya gabatar a gabanta a matsayin hujjar da za ta yi amfani da ita wajen korar karar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi.

A karshe alkalin kotun, Mai sharia Ibrahim Sarki Yola, ya ce kotu ta karbi rubutattun bayanan bangarorin kuma za ta sanar da kowannensu game da ranar da za ta yanke hukunci.