✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na ci karo da maciji a ganyen latas da na saya’

An kama macijin mai guba a yayin da ake shirin gyara latas din a yi girki

Wani mutum ya yi gamo da maciji a cikin ganyen latas din da ya sayo a wani babban shagon kasuwanci.

Bayan Mista Alex White ya bude ledar da ya sayo latas din a ciki ne a ranar Alhamis, ana shirin gyara latas din, sai ya ga wata halitta tana motsi a ciki.

Yana cikin al’ajabin yadda aka yi halittar da ya dauka katuwar tana ce ko tsutsar da bai taba ganin irinta ba ta shiga cikin ledar, kawai sai ya ga abin ya fito da harshe irin na maciji.

“Na yi mamaki da na ga ya zaro harshen nasa yana ta motsi; a nan ne na tabbatar cewa maciji ne sobada tsutsa ba ta fito da harshenta,” inji Mista White, mazaunin birnin Sydney na kasar Australiya.

Ya ce, “Gaskiya na dan kidime,” da ganin macijin a cikin latas din da na sayo, ga shi a babban shagon kasuwanci na yi sayayyar.

Daga nan sai ya kira jami’an tsaro, suka zo aka kama macijin; jami’an kuma gano cewa an dauko macijin ne a cikin ledar kunsa latas daga wani gidan sanyaya kayan ganye da ke birnin Toowoomba mai nisan kilomita 870 daga Sydney.

Suna zargin tsananin sanyin motocin daukar kayan ganyen ne ya sumar da karamin macijin har lokacin da Mista White ya sayi latas dinsa a shagon kasuwanci na ALDI ya sa a cikin jakarsa ta baya, ya tafi gida a kan kekensa.

Ya ce shi da mai dakinsa Amelia Neate sun ga macijin yana tafiya ne bayan da aka ciro latas din daga robar, ana shirin gyarawa.

Mutumin ya ce da suka lura cewa ledar ganyen ta huje yadda macijin zai iya guduwa, sai suka yi sauri suka samo roba suka rufe ganyen da macijin.

Daga nan suka kira masu kama maciji da masu ceto a waya, suka zo suka kama macijin da dare.

Kafin isowarsu, jami’an da sun shawarce shi da cewa idan har macijin ya sare shi, to ya yi gaggawar zuwa asibiti.

Shugaban kamfanin kama macizai na WIRES, Gary Pattinson, ya ce tsawon macijin ya kai Sentimita takwas, amma, “Dafinsa na da hatsari kamar sauran macizai masu dafi.”

Ya ce, “Karon farko ke nan da na taba ganin maciji a cikin kayan leda,” amma ya ce a baya “Mukan samu ga kwadi, lokaci zuwa lokac.”

Ya ce za su ci gaba da kula da macijin, sannan su mayar da shi gandun macizai an Queenslanda a mako mai zuwa, kamar yadda doka ta tanada.

Yanzu dai shagon kasuwanci na ALDI na binciken yadda aka yi macijin ya shiga cikin latas din.

“Muna aiki tare da kwastoman da kuma WIRES domin gano daga ina macijin ya fito, domin tabbas ba ALDI ba ne!” inji kamfanin na kasar Jamus, a cikin wata sanarwa.

Macijin da aka kama a gidan, wanda WIRES suka dauki hotonsa ranar 15 ga Afrilu, 2021.