✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na daina zage-zage a Soshiyal Midiya —Murja

Murja ta ce ta Saukar Al-Kur’ani amma ba ta san wakar ‘Cas’ ta Ado Gwanja ta saba doka ba

Fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi alkawarin daina zage-zage a zaurukan sada zumunta.

Murja ta yi alkawarin ne bayan Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke ta kan zargin yin zage-zage, batsa da kuma bata tarbiyya ta Soshiyal Midiya.

Matashiyar, wadda ake shirin gudanarwa a gaban kotu, ta shaida ’yan sanda cewa, ta yi saukar Al-Kur’ani, kuma daga yanzu, “A bangaren zagi na yi alkawari na daina.”

Da take amsa tambayoyin kakakin rundunar game da irin abubuwan da take yi a Soshiyal Midiya, wadanda al’umma ke tir da su, Murja ta ce, “Ai duk mai hankali ya san idan ya aika ba daidai ba.”

Amma a kan zargin ta da bata tarbiyya, cewa ta yi, “Da farko ni dai Murja ba waka nake yi ba balle in ce yara za su iya hawa wakata har tarbiyyarsu ta lalace.”

Game da zargin hawa wakokin batsa da makamantansu kuma, ta ce, “Gaskiya ni ba mace ba ce ma’abociyar yawan hawan wakokin batsa.”

A cewarta, ba ta taba sanin cewa wakar ‘Cas’ ta Ado Gwanja ta saba doka ba, shi ya sa ta hau wakar a Tiktok kuma ba ita ce farau ba.

“Har ga Allah ban san wannan wakar tasa ta saba doka ba, saboda yadda na ga mutane na amfani da wakar (a Tiktok) ya sa ni ma na hau wakar,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa ta fara cin karo da wakar Ado Gwanja ta ‘War’ ce a Soshiyal Midiya, kuma kafin ita dubban mutane sun hau wakar.

Wakojin biyu (Cas da War), sun tayar da kura, kan zargin yada badala, har Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar NBC ta haramta sanya su a gidajen rediyo da talabijin.

A kan wakokin ne kuma wasu lauyoyi masu kishin jihar Kano suka maka Ado Gwanja a kotu kan zargin lalata tarbiyya.

Tabara a Soshiyal Midiya

A yayin amsa tambayoyin mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Murja ta bayyana dalilan da suka sa take yin ashariya a bidiyon da take wallafa a Soshiyal Midiya.

Zage-zage

A cewar Murja, “maganar gaskiya game da zage-zage da na yi, zagi ne wanda na yi tun kafin a neme ni a wannan kotun ka karar da malamai suka shigar.

“Shi wannan zagi na farko abin da ya sa na yi shi akwai abin da ya faru wanda bidiyon wasu mata da ’ya’yansu da aka kama na gansu a wani daji, a lokacin mun yi roko don Allah don Annabi a taimaka a shiga lamarin wadannan mata da ’ya’ya a daji saboda iyaye ne.

“Shiru-shiru, sai abu ya kara rikicewa na ga an dauko bulala ana dukan wata mata da kananan yara a daji wanda hakan ya sa hankalina ya tashi na rika rusa ihu, na rasa abin da ke min dadi, na rasa ‘control’ dina na fito na rika wannan zage-zagen a kai.

“Zagi na biyu shi ne, wanda ya dauko hotona ya ce na rasu. Wannan ya sa aka kira ni a waya aka ce mini ai wani ya wallafa a soshiyal midiya, lokacin farkon fara Tiktok dina ne, ya wallafa cewa mun yi hatsari a hanyar dawowa ta daga Kaduna.

“An fada wa babarmu cewa mun yi hatsari na rasu, babarmu ta yanke jiki ta fadi na rasa ‘control’ dina shi ma na fito na yi zagi a kan wannan abun.

“Da na dawo gida sai da [aka] dauki awanni sosai wanda kowa ya san wannan, kafin mahaifiyata ta farfado.

“Daga wannan zagin guda biyu da na yi, tun daga lokacin da irin kalubalen da na fuskanta ka san a rayuwa wasu ba za su fahimci mene ne ya sa ka yi zagin ba, kai da ake gani laifinka za a gani.

“Na yi wa mahaifina alkawarin in Allah Ya yarda ba zan kara zagi a kan irin wadannan abubuwan ba.”

Badala a Soshiyal Midiya

Game da sauran kalaman ta a Soshiyal Midiya da ke nuna rashin tarbiyya da batsa, mastahiyar ta ce ce: “Wakoki da ake magana a kaina, wakoki ne na Ado Isa Gwanja. Wanda na farko ya saki ‘War’, sai ta biyu ‘Cas’.

“Ita wannan War din da ya saki sama da mutum wajen dubu nawa sun hau, ina bibiya a Tiktok na hadu da ita ni ma na bi na hau wakar.

“Sai kuma ita Cas din, wanda mun yi waya da shi Ado Isa Gwanja ya ce na saki wakata.

Har ga Allah ban san wannan wakar tasa ta saba doka ba saboda yadda na ga mutane na amfani da wakar (a Tiktok) ya sa ni ma na hau wakar,” in ji Murja.

Game da matakin karatunta na addini da boko, Murja ta ce: “Na yi sauka a matakin karatun addini; Na Boko kuwa ban gama sakandare ba na daina.”

Ga ci gaba hirar tasu:

Kiyawa:  Kina ganin irin wadannan bidiyo da kike wanda akwai alamun rashin tarbiyya a cikinsu, kina ganin daidai ko ba daidai ba?

Murja: Gaskiya duk mutum mai hankali, akwai abin da idan kana yi kai da kanka ka san cewa ba daidai ba ne.

Amma duk mai bibiyar shafukana yana kallo ya san ina da ra’ayi irin na Allah ka kawo mana mafita a kan mu daina abubuwan da muke yi a soshiyal midiya.

Don ba na mantawa ko mako daya ba a yi ba sanadiyyar rasuwar da aka yi mana ta Kamal Aboki, na wallafa sako nake cewa Ya Ubangiji idan wata lalura ce za ta zama sanadiyyar shiryuwata ni Murja duba da yadda na ga Kamal ya rasu ana tare, Allah Ka dora mini wannan cutar.

Kiyawa: Ko kina nadamar abubuwan da kika yi wadanda suka shiga kafafen sada zumunta na zamani wanda za a iya cewa kusan har abada suna nan har ’ya’ya da jikokinki za su gani?

Murja: Abin da zan iya cewa shi ne, a bangaren zagi na yi alkawari na daina, da ma shi ne babban kalubale a rayuwa.

Kiyawa: Sauran bidiyo na yada batsa da makamantansu kuma fa?

Gaskiya ni ba mace ba ce ma’abociyar yawan hawan wakokin batsa.

Kiyawa: Yanzu za a ci gaba ke nan ko ya abin yake?

Murja: Tun kafin ma a kawo wannan martanin, tun a rasuwar da aka yi kamar yadda na fada a baya a kan mutuwar Kamal na ce, ko da wata lalurar ce za ta yi sanadiyyar shiyuwata Allah Ka nuna mini ita.

Kiyawa: A baya an samu rahoto a kanki cewa kin ce ’yan sanda ma ba su isa su kama ki ba, mene ne gaskiyar wannan lafazi da mutane ke ta yawo da shi a gari?

Murja: Maganar Allah karya ce. Kuma hujjata, bidiyoyi ne suke yawo a gari.

Kiyawa: Yanzu me kike tunani za a rika gani daga gare ki, ko za ki rika wallafawa nan gaba, misali bayan an kai ki kotu?

Murja: Abin da zan rika wallafawa shi ne gaskiya, maganar Allah, zan kara maimaitawa babban kalubalen da nake fuskanta a Soshiyal Midiya shi ne zagi kuma na riga na yi alkawarin daina shi.

Idan aka duba bidiyona na baya da wata daya ina yawan magana a kan na daina zagi. Hasali ma akwai wanda fada ya hada mu da shi kwanan nan.

Kiyawa: Kina ganin wannan kamun na ki zai iya sanadiyyar shiryuwarki na wadancan abubuwan da ake ganin ba daidai kike yi ba, kina abubuwan da yara masu tasowa za su kwaikwaya alhali ba abu ne mai kyau ba a ala’adar Hausawa da kuma Musulunci?

Murja: Da farko ni dai Murja ba waka nake yi ba balle in ce yara za su iya hawa wakata har tarbiyyarsu ta lalace.

Magana dai a kan zagi ne, zagi kuma tun kafin a kai wannan mataki ina yawan fadin na daina zagi insha Allah saboda yadda mahaifina ya nuna min.

Kiyawa: Wani sa’in idan kika fito kina wasu abubuwan sai a ga kamar kwakwalwarki ce ta dan samu matsala ko kuma dai wani abu, akwai bakin iyaye ne ko kuma makamancin haka?

Murja: Allah Ka rabu da bakin iyaye. Allah Ka kare mu. Ina zaune da iyayena lafiya.

Kiyawa: To maganar kwakwalwar fa?

Murja: Kwakwalwata lafiya lau, kawai ‘content’ dina [ne] a haka na soshiyal midiya.”

Dalilin kai karar Murja

Malamin da ya shigar da kara, Mu’azzam Sulaiman Khalid, wakilin zauren hadin kan malamai na Jihar Kano, ya bayyana dalilin yin karar matashiyar.

“Abin da yake akwai shi ne a irin yanayin jarrabawar da muka sami kanmu harkoki na kafofin sada zumunta na zamani (Tiktok), an samu wata yarinya mai suna Murja wadda ta yi wasu maganganu wadanda suke kai-tsaye sun saba wa tarbiyya ta Addinin Musulunci da kuma zamantakewarmu.

“Abin da zai iya zama hadari ga ’yan baya, saboda haka muka ga ya kamata hukuma ta shiga cikin lamarin.

“Sannan a matsayinta na ’ya mace, muna fatan Allah Ya sa ta gane kuskurenta ta dawo kan daidai.”

Barista Badamasi Suleiman Gandu, lauyan zauren malamai na Jihar Kano, ya ce, “Abin da yake akwai, akwai samarin lauyoyi masu kishin addini da tarbiyyar Islama kasancewar wannan badalar da take yawa a soshiyal midiya wanda ya biyo bayan wakoki na rashin mutunci da zage-zage, musamman wadda aka kama, Murja Ibrahim Kunya take yi muka kai korafi ga kotu kuma kotu ta ba da umarni da a zo a kama ta ko a kama su, a bincike ta ko a bincike su sannan a gurfanar da su a gaban kotu.

“Cikin ikon Allah, jiya Allah Ya ba da nasara an kama ta, kuma bincike yana gudana.

“Don haka abin da muke yi da farko muna yaba wa hukumar ’yan sanda bisa kokarin da suke bayarwa wajen dakile wannan badalar.

“Da fatan za a yi abin da ya kamata na adalci, kuma a maida ita kotu kamar yadda kotu ta yi umarni da a bincika a maida mata.”