✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fi cancanta in zama shugaban PDP- Secondus

Mista Uche Secondus, mai fafutukar neman shugabancin Jam’iyyar PDP, ya ce shi ne ya fi cancanta da shugabancin jam’iyyar. Secondus ya taba rike shugaban jam’iyyar…

Mista Uche Secondus, mai fafutukar neman shugabancin Jam’iyyar PDP, ya ce shi ne ya fi cancanta da shugabancin jam’iyyar.

Secondus ya taba rike shugaban jam’iyyar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, sannan kuma ya rike mataimakin shugaba, da kuma shugaban jam’iyyar reshen Jihar Ribas.

“Idan na zama shugaban jam’iyyar, zan yi aiki da kowa. Tun daga jam’iyyar ta kasa har zuwa mazabu 9,000 da muke das u a kasar domin mu samu nasarar lashe zaben 2019,” inji shi.

Secondus kuma ya yi alkawarin cewa zai kawo kuri’un Jihar Ribas, da kuma yankin baki daya a zabuka masu zuwa.