✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gudo karamar yunwa na fada babba a Najeriya — ’Yar Nijar

Yashi Ghali ’yar asalin Jihar Tawa ce da ke Jamhuriyar Nijar, wadda ta shafe sama da shekara 20 a Najeriya, inda ta zauna a jihohin…

Yashi Ghali ’yar asalin Jihar Tawa ce da ke Jamhuriyar Nijar, wadda ta shafe sama da shekara 20 a Najeriya, inda ta zauna a jihohin Arewa da dama ciki har da Kano da Zariya da Kaduna da Minna. Yashi Dattijuwa ce mai kimanin shekara saba’in.

Ta ce ta shigo Najeriya ne tare da ’yarta daya da ta tsira da rai cikin ’ya’ya bakwai da ta haifa.

Yashi ta hakura da mazauninta na yanzu da ke Unguwar Ikwa a garin Zuba Abuja inda take da zama da ’yar tata sai kuma jikokinta 5 maza da ’yarta ta haifa.

Ta ce baya ga wadannan jikoki mazan 5, akwai kuma jikokinta mata uku da ’yar tata ta haifa da ke gidajensu na aure a Abuja da Jihar Neja da kuma Kaduna.

Tana zaune ne a gidan da daya daga cikin mijin jikokin nata ya zaunar da su. Aminiya ta yi kicibis da ita a garin Kubwa Abuja, inda ta je yawon bara tare da daya daga jikokinta maza, inda ta yi masa bayani a kan rayuwarta.

Yunwa ta sa na baro kasarmu Nijar

Aminiya ta tambaye ta dalilin da ya sa ta baro kasarta Nijar, ta zauna a Najeriya.

Ta ce “Yunwa ce ta koro ni daga Nijar na zo Najeriya don neman abin da zan ci.”

Ta ce mijinta ya jima da rasuwa kuma ta zo kasar nan ne tare da ’yarta da kuma surukinta.

Ta ce a baya takan ziyarci gida Nijar a kai-a kai, sai dai rashin walwala ya sa ta takaita ziyarar a yanzu, a sakamakon rashin abin hannu.

Yashi ta ce sai dai lamura sun juya a Najeriya a yanzu inda samun abin da za ta ci a kullum yake zame mata babban kalubale, sabanin baya lokacin da ta ce ta fi samun abin hannu saboda yanayin walwala da ake ciki a wancan lokaci.

“Yunwa ta sa na bar kasata Nijar, sai dai a Najeriyar ma a yanzu ba kudi da yawa sai mutuum ya fita a kullum, idan ka sami kamar Naira dubu biyu, ka sayi shinkafa mudu guda ragowar bai wuce na mota ba da kuma na abin da za a hada abincin da shi,” inji ta.

Ta kara da cewa yanzu Najeriyar ma tana fama da yunwar da ta sa ta baro kasarta ta Nijar a can baya. Sai dai ta ce tun lokacin da ta zo Najeriya kimanin shekara 20 da suka gabata, ta ziyarci gida Nijar kamar sau biyu ne kafin ta hakura da ziyarar saboda yanzu tana cikin matsin rayuwa da neman na abinci take a kullum kafin ta samu, ballantana har ta yi tunanin tara kudin da za ta yi kudin mota zuwa kasarta Nijar din.

Ta ce hakan ya sa yanzu take yi wa kanta kallon ’yar Najeriya ce ita ma kamar sauran wadanda aka haifa a kasar.

Yadda surukina ya sama mana gidan zama

Aminiya ta ziyarci gidan da Yashi ke zaune da ’yar tata da kuma jikokinta biyar a Unguwar Ikwa a garin Zuba Abuja, inda ta gane wa kanta yanayin rayuwar da Yashi ke ciki da jikokinta da ’yarta A’isha.

Gida ne da surukinta da suka rabu da ’yarta ya saya mata a baya, ya kuma bar musu domin su ci gaba da rayuwa duk da sun rabu na tsawon lokaci.

Aminiya ta zanta da ’yarta din mai suna A’isha.

Ta ce yawancin ’yan kabilarsu (Buzaye) suna barin kasarsu ta asali ne saboda dalilai da dama da suka hada da rashin abin yi a can kasar kamar rashin rakuma da suke kiwo, ko rashin jarin kasuwanci da kuma rashim samun damar yin karatu da zai ba mutum damar yin aikin gwamnati.

“Wannan ne yake tursasa mutanenmu da dama su bar kasarmu su dawo nan Najeriya da zama, mu samu wani abin yi kamar aikin gida da makamantansu domin samun abin sakawa a bakin salati,” inji A’isha.

Ta ce sai dai a yanzu tuni ta rabu da mijinta, wanda suka zo kasar nan tare kafin shi ya koma gida Nijar. Ta ce a yanzu ita ce ke matsayin uwa da kuma uba ga ’ya’yanta.

Ta ce aurenta da mijinta da suka zo kasar tare ya rabu ne, inda shi kuma ya koma kasarsu Nijar da zama ya barta da yaran da suka haifa.

Ta ce sai dai a yanzu ta fara tsoro da yadda lamura suka koma a kasar nan, musamman na rashin zaman lafiya da ke addabar kasar na kashe-kashe da sauransu, wanda ke jefa kasar cikin yanayi na rashin tabbas da tsananin rayuwa.

A’isha ta aurar da ’ya’yanta a nan Najeriya kuma da yawansu suna zaune a gidajen aurensu lafiya har sun hayayyafa.

A game da babban abin da ba za ta taba mantawa da shi ba a rayuwarta kuwa, sai ta ce babban abin alherin da ya same ta da ba za ta taba mantawa da shi ba, shi ne gida, wanda daya daga cikin surukanta ya ba ta a garin Zuba, inda take zaune tare da mahaifiyarta da kuma ’ya’yanta maza biyar.

“Duk da cewa na jima da rabuwa da mijina wajen shekara takwas ke nan a yanzu, sai dai mahaifinsu kan ziyarce mu lokaci bayan lokaci. Zuwansa na karshe shi ne lokacin Babbar Sallar bara, inda ya yi kusan mako biyu a nan tare da yaran.

“Sai dai ni na zabi zama da yaran nawa a maimakon da shi saboda matsalar da ta raba mu na rashin kula da hidimarsu, har yanzu tana nan ba sauyawa za ta yi ba.

Ya kula da iyalansa na can gida, ni kuma zan zauna da wadannan a nan, ya fi mini kwanciyar hankali,” injita.

Burina na yi karatu zuwa jami’a – Jikan Yashi

Aminiya ta kuma zanta da daya daga cikin jikokin Yashi mai suna Mustafa Muhammad da ke babbar makarantar sakandare a yanzu da kuma ta koyon sana’ar dinki.

Ya ce ya taba ziyartar Nijar sau daya a rayuwarsa.

Ya ce burinsa shi ne ya yi makaranta har zuwa matakin jami’a tare da yin aiki ko kasuwanci ko sana’a da zai kyautata rayuwar iyaye da kuma iyalinsa.