✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Na kai shekara 60 ina sana’ar kamu’

Dattijuwa ‘Na yi aikin Hajji na aurar da ’ya’ya mata da sana’ar kamu’

Hajiya Hadiza Saje Wada mai kamu da ke Kwarin Gogau Tudun Wada Zariya, ta kwashe shekara 60 tana sana’ar sayar da kamu har yanzu tana ci gaba da sana’ar duk da cewa yanzu haka tana da shekara 100 a duniya.

A zantawarta da Aminiya, Hajiya Hadiza ta ce ta fara sayar da kamu a lokacin ana sayar da buhun gero fam daya, tiyar geron ba ta wuce kwabo biyu ko ahu.

Ta ce a wancan lokaci ba mai iya sayen kamun kwabo biyu sai dai na kwabo daya ko anini ko ahu.

Hadiza Mai kamu ta ci gaba da cewa amma saboda yanayi ya canja buhun gero har ya kai sama da Naira dubu 25, a yanzu kamu daga Naira 50 sai zuwa sama.

A cewarta, sana’ar kamu ta yi mata komai saboda ta je aikin Hajji ta aurar da ’yan mata kuma har yanzu tana cikin rufin asiri.

Ta ce duk da kasancewar ita Bakatsiniya ce, amma ta yi fice a fagen sana’ar kamu wadda Nupawa aka san su da ita.

Sai ta kara da cewa dalilin zaman aure ne ya kai ta gidan Nupawa, kuma surukarta ce ta koya mata yadda ake sarrafa kamu tun a lokacin babu injin nifa sai dai dutsen nika da mata ke amfani da shi wajen sarrafa duk wani abin da yake bufatar haka.

Ta ce mijinta marigayi Alhaji Saje Wada ne ya auro ta ya kawo ta garin Zariya a lokacin Sarkin Zazzau Ibrahim yana mulki.

Dattijuwar ta shawarci mata su nemi sana’ar yi a gidajen mazansu domin taimaka wa kansu da kuma ’ya’yan da za su haifa da kuma mazansu.

Ta ce yawace-yawacen bara da wadansu mata suke sa kansu a wannan zamani ba su dace da dabi’un mutanen Arewa ba domin matan Arewa an san su da kunya da kuma kamun kai.