✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na kasa mancewa da mijina…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin. Ga ci gaban labaran…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin. Ga ci gaban labaran auren wasu daga cikin masu karatu don amfanar da mu gaba daya:

Na kasa mancewa da shi.

Malama Nabila na kasance ina cikin tsakiyar aljannar duniyar jin dadin zaman aure, kwatsam sai masu garkuwa da mutane suka fado mana cikin tsakiyar dare suka katse wannan jin dadin.

A ranar ni ke da aiki, yana daki muna tare suka balle kofa suka shigo, suka harba masa bindiga ya fadi ya mutu a gabana jikina na karkarwa suka kuma bi da adda suka yanka wuyansa.

Na kadu sosai na shiga yanayi na firgita sosai. Na kasa mancewa da shi da tunaninsa nake kwana da shi nake tashi, da wuya in yi barci in farka ban yi mafarki da shi ba. Shekarata uku ke nan da rasuwarsa amma kullum sai na dora hotunansa a sitatus ina kewarsa ina masa addu’a.

Yanzu al’amarin ya fara damun ’yan uwana suna ganin abin yayi yawa wai ya kamata in mance da shi, in bude zuciyata in ba wani dama ya shiga don in yi aure tunda dai har yanzu akwai sauran yarinta a tare da ni.

Ba kamar wata kanwar mahaifina wacce tun ina hakura da fadan da take min, har abin ya fara kule ni. Domin ta sha tara mitin a kaina wai a yi min fada in mance da tsohon mijina.

A wajen mitin na karshe na cire kunya na ce ku ma kun san Maigari ba mijin da za a manta da shi ba ne komai yawan shekaru, kuma aure sai dai in yi don neman lada da tsaron mutunci amma mawuyacin abu ne in kara samun miji, namijin duniya kamar Maigari.

Kowa ya tuna bara…

Ina aji hudu na sakandare kakanmu ya hada mu auren zumunci da dan wan babanmu. Dama can akwai shakuwa da fahimtar juna sosai a tsakaninmu. Shi nake zuwa wajensa yana koya min karatun da aka ba mu mu yi daga makaranta.

Lokaci da na fara yin samari kuwa, shi nake ba labarin samari, in ce masa ba na son wane da wane saboda kaza da kaza, amma ga wanda nake so, ya yi ta ba ni shawara.

Ya kasance ya grime ni sosai, ya ba ni wajen shekara ashirin. Lokacin da kakanmu ya hada wannan auren zumuncin ba na son sa saboda akwai wanda nake so a zuciya, amma ba yadda zan yi saboda ban zan iya yi wa mahaifina tawaye ba, shi kuma kakanmu dama duk abin da ya gindaya ba wanda ya isa ya ketare kaf a cikin danginmu.

Haka nan ina ki ina bore aka daura mana aure da Maigari cikin wata hudu kadai da fara maganar. uwargidansa a lokacin ta ta da bore ta ce ba za ta yi kishi da ni ba karshe sai da ya kai ga mutuwar aure a tsakaninsu.

Saboda yadda ya rika kyautata mani da nuna kauna da kulawa da kokarin jiyar da ni dadi da sa ni farin ciki, cikin wata uku na samu kaina tsundum cikin kogin so da kaunar Maigari, ta yadda koyaushe ina cikin tunani da begensa, kuma ni ma haka na fara kokarin kyautata masa da nuna kauna da kulawa gare shi.

Ban dade da yin haihuwar farko ba ya kara auro wata matar. Haka muka yi rayuwar aurenmu wannan ta zo wannan ta fita sai da na zauna da kishiya guda tara, amma ni ko yaji ban taba yi.

Ana ta cewa na mallake shi ya sa ba na samun matsala da shi. Amma kuma ni na san abin da ya taimake ni shi ne zaman gaskiya tsakani da Allah da kuma babban lakanin da mahaifina ya yi min wasiyya da shi cewa duk abin da mijina ke so, in dai bai saba wa shari’a ba, to ni ma in so shi.

Na zauna da Maigari, don tsananin ladabi da biyayya in Maigari ya ce wannan abin fari ne, to kada kuwa baki ne haka nan zan amince in ce masa fari.

Sai mako na gaba za mu ji karashen wannan labari in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.