✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na kashe mutum 10 —Dan kungiyar asiri

Dan kungiyar asirin ya bayyana yadda ya aikata kisa.

‘Yan sanda sun gurfanar da wani mutum da ake zargi da kashe wani a yayin aikata fashi da makami a Benin, babban birnin Jihar Edo.

Wanda ake zargin mai shekara 24, dan kungiyar asiri ne, ya hada baki da ‘yan kungiyarsa suka yi wa mutumin fashin suka kuma jefar da gawarsa cikin Kogin Ikpoba.

“Mun yi masa dabara ne  muka daki motarsa ta baya shi kuma ya fusata ya biyo bayanmu.

“Abokaina sun tafi da katin cirar kudi da muka kwata a wajensa.

“Bayan tafiyarsu ya kama ni da kokawa, ni kuma kawai na daba masa wuka na jefa gawarsa cikin kogi”, inji wanda ake zargin.

Ya fadi haka ne a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida, inda ya bayyana yadda ya kashe wani mutum.

Da aka tambaye shi adadin mutanen da ya kashe lokacin da yake kungiyar asiri, matashin ya ce ya kashe sama da mutum 10.

Har wa yau, ‘yan sanda a jihar sun cafke wani mai shekara 50 da ke da hannu a kona ofishin ‘yan sanda a birnin Benin yayin zanga-zangar #EndSARS.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Johnson Kokumo, ya ce wanda aka kama din ya samo man fetur ne tare da cinna wa ofishin ‘yan sandan wuta.

Ya gargadi bata-gari a jihar cewa rundunar ba za ta saurara wa duk wanda aka kama da aikata laifi ba.