✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na kece da dariya da na ji kulob din Arsenal na zawarcina – Benzema

Shahararren dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid na Sifen Karim Benzema ya ce sai da dariya ta kwace masa a lokacin da ya…

Shahararren dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid na Sifen Karim Benzema ya ce sai da dariya ta kwace masa a lokacin da ya samu labarin kulob din Arsenal na Ingila ne nemansa.

Kocin Arsenal Arsene Wenger dai yana zawarcin dan kwallon gaba ne inda ake hasashen zai yi cefane a watan Janairun 2016 idan aka bude kasuwar saye da kuma sayar da ’yan kwallo. Rahotanni suka nuna kocin yana tunanin dauke dan kwallon Madrid na Sifen ne musamman ganin yadda dan kwallon gabansa Danny Welbeck ya ji rauni yayin da Theo Walcott da Oliber Giroud kuma suka yi sanyi a bangaren zura kwallo a raga.
Benzeama ya ce abin ya ba shi dariya da ya ji wannan rade-radi na komawarsa Arsenal, inda ya ce ta yaya zai bar kulob din Madrid wanda ya fi kowane kulob a duniya sannan ya koma na kasa da shi.
Jaridar Daily Mirror ta Ingila ta ruwaito dan kwallon ya bayyana cewa idan ka cire kulob din Madrid da na FC Barcelona dukkaninsu da ke Sifen, babu wani kulob da ya kama kafarsu a duk fadin duniya, don haka bai ga dalilin da zai sa ya bar kulob din da yake samun nasara ba ya koma na kasa da shi.
Kawo yanzu Benzema yana haskakawa a kulob din Madrid, sai dai yana jinyar makwanni uku saboda raunin da ya samu. Alamu sun nuna da wuya kuilob din Madrid ya sayar da shi ganin yadda kulob din bai da magajinsa.