✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na matsu na bar mulki – Buhari

Wannan ba shi ne karo na farko da Buhari yake nanata hakan ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake nanata cewa ya matsu ranar 29 ga watan Mayu ta yi, ya mika mulki.

A lokuta da dama dai a baya, Buhari ya sha nanata cewa ya matsu ya mika mulki ga wanda zai gaje shi.

Buhari dai zai mika mulki ne ga Bola Tinubu, zababben Shugaban Kasa da ya lashe zaben watan jiya, a karshen watan na Mayu.

Sai dai da yake jawabi yayin wani taron bankwana da Jakadiyar Amurka a Najeriya, Ambasada Mary Beth Leonard, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, Buhari ya ce ya matsu ya tafi.

Shugaban ya ce yana sa ran kasancewa babban makiyayin da zai ci gaba da lura da gonarsa mai shanu sama da 300 da ke Daura, a Jihar Katsina.

Buhari, wanda kuma ya jinjina wa ’yan Najeriya a zabukan da suka gudana, ya kuma ce yanzu Dimokuradiyyar kasar ta girma.

Ya ce, “Mutane yanzu sun fara gane ikon da yake hannunsu. Kasancewar an ba su damar zaben wanda suke so, babu wanda zai ce musu ga abin da za su yi.

“Ba na farin cike da cewa wasu ’yan takara sun fadi, amma na ji dadin yadda mutane suka sami damar tantance wanda suke so ya shugabance su.

“Sakamakon canjin kudin da aka yi, babu isassun kudin da ’yan siyasa za su raba, amma duk da haka na fada wa mutane su karbi kudin su zabi wanda suke so,” in ji Buhari.

Ya kuma ce ya gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba tare da wani katsa-landan ba daga ko’ina.