✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na sa an sace babana an kashe shi, aka ba ni N2,000 —Dan bindiga

Matashi dan bindiga ya bayyana yadda suka addabi yankin Zariya.

Dubun wani matashi ta cika bayan ya sa an yi garkuwa da kanin mahaifinsa aka kashe shi bayan karbar kudin fansa a yankin Zariya, Jihar Kaduna.

Matshin, mai shekara 30, mazaunin kauyen Tankarau da ke gundumar Dutsen Abba a Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, ya ce Naira dubu biyu kacal aka taba ba shi a ayyukan garkuwa da mutane da suka yi tare abokansa ’yan bindiga a yankin Zariya. Ga bidiyonsa a kasa.

“Na dauki lambar kanin babanmu na ba Ayuba, ya tura wa Isah, aka je aka kashe shi, shi ne wanda na yi sanadiyya.

“Sauran duk wanda zan lissafa muku kiran mu ake yi. Kiran su ake yi,  ni ma sai su kira ni mu je a yi.”

– Hare-haren da muka kai a Zariya –

Ya bayyana cewa su ne suka kai hari Asibitin Kula da Cutar Kuturta da Tarin Fuka da ke Saye, wanda ya ce an ba shi ladar Naira dubu biyu.

“A na ‘Leprosy’ (asibitin kutare) sun ba ni N2,000, suka ce in suka je duk yadda ake ciki zan ji.

“Da suka je, [bayan] kwana biyu na kara kiran su, [sai] suka ce min idan ina da karfi in zo in karba,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Ko sisi ba a ba ni ba, wannan dubu biyu da aka ba ni a ‘Leprosy’ shi ke nan abin da aka ba ni.”

Ya bayyana hakan ne a lokacin da manema labarai suke masa tambayoyi a ofishin rudunar ’yan sanda ta musamman da ke yaki da ayyukan ta’addanci da satar mutane (IRT) da ke Zariya, inda ake tsare da shi.

Ya tabbatar wa ’yan jarida cewa shi ne ya jagoranci ’yan bindiga zuwa gidan Farfesa Aliyu Mohammed Wazirin Wusasa, wanda suka kashe dansa a harin, shi kuma suka tafi da shi sai da aka biya su kudin fansa Naira miliyan 20, bayan mako uku.

Matashin ya bayyana cewa gungunsu ne suka kai hari a unguwar Zangon Shanu, inda suka sace wata likita mai juna biyu, suka kashe ta a hanya bayan ta kasa tafiya.