✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na samu sabon masallacin da zan ci gaba da limanci – Sheik Nuru Khalid

Ya ce zai fara jan sallah ne a masallacin daga Juma’a mai zuwa

Tsohon babban limamin Masallacin Juma’a na unguwar ’yan majalisa da ke Apo a Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya ce ya samu sabon masallacin da zai ci gaba da jan sallah.

Sanarwar na zuwa ne a ranar da Kwamitin Masallacin na Apo ya sanar da sallamar shi gaba daya, bayan ya dakatar da shi tun da farko.

A karshen makon nan ne dai Kwamitin Masallacin, karkashin Sanata Sa’idu Dansadau ta fitar da sanarwar dakatar da malamin daga limancin saboda hudubarsa ta ranar Juma’a a kan matsalar tsaro.

To sai dai Sheikh Nuru ya ce tuni Kwamitin Gudanarwar sabon Masallacin Juma’ar da aka gina a unguwar ma’aikatan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ba shi limanci a can.

Ya ce zai fara jagorantar sallah ne daga ranar Juma’a, takwas ga watan Afrilun 2022 mai zuwa.

Ya ce, “Da yardar Allah zan fara jan sallah a sabon masallacina ranar Juma’ar nan mai zuwa, saboda a matsayinmu na limamai, dole sai mutum ya samu wajen da zai rika limanci.

“Akwai sabon masallacin da muka gina a bayan unguwar CBN, ni ne zan rika jan sallah a can,” inji shi.

Malamin dai ya bayyana sallamar da aka yi masa daga masallacin na Apo a matsayin kaddararsa, saboda ya fadi gaskiya.

A yayin hudubar tasa dai, malamin ya kalubalanci gwamnati mai ci kan yadda ya ce ta gaza magance matsalar tsaron da ya addabi al’umma, musamman ma a kan harin jirgin kasan da aka kai a tsakanin Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.