✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na samu sauki —Maryam Yahaya

Cutar zazzabin cizon sauro da Typhoid ne suka addabi jarumar.

Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, Maryam Yahaya ta sanar da cewa ta samu sauki da rashin lafiyar da addabe ta.

Kusan wata daya ke nan ana ta rade-radin cewa jarumar tana fama da matsanancin rashin lafiya, inda mutane da dama suke cewa asiri aka mata.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jarumar, amma ba ta dauki waya ba, sai dai ta wallafa a shafinta na Instagram cewa ta samu sauki.

A cewarta, “ku saurari hirar da na yi da BBC Hausa akan rashin lafiyata. Alhamdulillah na samu sauki. Na gode ga wadanda suka yi min addu’o’i da wadanda suka zo har gida domin dubani. Jazakamullahu khairan.”

A hirarta da BBC Hausa, ta bayyana cewa malariya da typhoid ne suke damunta, kuma ta samu sauki, sai dai kawai jikinta babu karfi.