✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na tafka kuskure a tafiyar Buhari, ba zan maimaita da Tinubu ba — Naja’atu

Naja'atu ta ce Buhari ya gaza cika alkawuran da ya daukar wa 'yan Najeriya.

Yayin da zaben Shugaban kasa na 2023 ke kara karatowa, tsohuwar Darakta a Kwamitin Yakin Zaben Bola Tinubu, Naja’atu Muhammad, ta ce ta tafka kuskure a tafiyar Shugaba Buhari a baya kuma ba za ta maimaita hakan a tafiyar Tinubu ba.

Naja’atu ta ce ta goyi bayan Buhari ido rufe ba tare da wasu kwararan abubuwa da za yi wa kasa ba.

Naja’atu ta bayyana haka ne cikin wata hira da gidan talabijin na Trust TV, inda ta ce Buhari ya karya gaskiyar da ke tsakaninsu.

“Mun yi tafiyar Buhari kuma miliyoyin mutane sun shiga tafiyarsa saboda muna tsammanin zai sauya Najeriya. Ba mu taba kai masa wasu bukatu na karan kanmu ba face alkawari da muka yi da shi kan abubuwan da zai yi mana, amma yau ga inda muka tsinci kanmu.

“Buhari ya yi watsi da ainIhin magoya bayansa, ba damu ya je Villa ba. Sannan duk alkawuran da ya yi na magance talauci, cin hanci da rashawa duk bai cika su ba.

“Yana shugabantar gwamnatin da ta fi kowa yin rashawa a tarihi, ya yi wa wadanda suka aikata manyan laifuka afuwa. Za a yi mutum ya saci miliyoyin kudi amma a haka maganar za ta bi ruwa.

“Yanzu haka muna jin rade-radin an sace wasu tiriliyoyin kudi, amma babu abin da ya ce, Buhari ya gaza cika alkawuran da ya daukar mana, Buhari ya gaza. Na yi kuskure a tafiyar Buhari don haka ba zan sake maimaita irinta da Asiwaju ba.”

Ta bayyana cewar Tinubu ya shaida mata cewar bai tanadar wa Arewa komai ba har ya ci zabe.

Kazalika, ta ce ba ta san cewar Tinubu ba shi da cikakkiyar lafiya ba sai da ta gamu da shi a birnin Landan.