Na yi nadamar goyon bayan Buhari a 2015 – Dino Melaye | Aminiya

Na yi nadamar goyon bayan Buhari a 2015 – Dino Melaye

Sanata Dino Melaye
Sanata Dino Melaye
    Sani Ibrahim Paki

Tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattijai ta takwas, Sanata Dino Melaye ya ce ya yi nadamar goyon bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayin zaben 2015.

Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Politics on Saturday na gidan talabijin na Channels ranar Asabar.

Sai dai ya ce jam’iyyarsu ta PDP na da kwarin gwiwar lashe zaben Shugaban Kasa me zuwa na 2023.

A cewarsa, “Da farko dai ina neman gafara daga Allah da kuma ’yan Najeriya saboda yadda na goyi bayan Buhari. Babu wata damfara da aka yi wa ’yan Najeriya sama da ta yada manufofin Buhari. Babu wata damfara da ta wuce wannan a tarihin Afirka ma gaba daya

“A da ni makaho ne, amma yanzu na warke. Ta yaya mutum zai zauna a cikin waccan jam’iyyar ko ya ci gaba da goyon bayansu duk kuwa da irin abubuwan da suke faruwa a kasar nan? Ta yaya? Gaskiya ni kaina yanzu nadama nake yi, an damfare mu,” inji Sanata Melaye.

Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar APC mai mulki ba abar amincewa ba ce, yana mai cewa ba ta da alkiblar siyasa ko ta ci gaban Najeriya kwata-kwata.

“Na yi makamantan irin wadannan kalaman lokacin ina cikin APC, amma kasancewata Kirista, kuma wanda ya imani da cewa littafin Baibul gaba yake da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kuma ya yi magana a kan duhu da haske, dole ta sa na fice na bar jam’iyyar.”