✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na yi tsammanin ni ne na mutu!

Na yi tsammanin ni ne na mutu.

Wani malalacin matashi ne ba ya da lafiya, aka kai shi asibiti, likita ya ba shi gado.

Bayan kwana biyu ya warke, amma wai saboda lalaci sai ya kara langabewa, don a ci gaba da tarairayarsa.

Ana nan sai wani majinyaci na kusa da gadonsa ya mutu, ’yan uwansa suka fara kuka, suna cewa; Allah jikan wane.

Shi kuma yana barci, sai ya ji ana wannan maganar samasama.

Da ya farka firgigi sai ya ruga da gudu.

Da aka tambaye shi ko lafiya? Sai ya ce: “Na yi tsammanin ni ne na mutu.”