✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nada Dan-Agundi da Ciroman Kano ya tayar da kura

Ana ci gaba da mayar da martani kan matakin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, na dawo da tsohon Sarkin Dawaki Mai Tuta, Aminu Babba…

Ana ci gaba da mayar da martani kan matakin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, na dawo da tsohon Sarkin Dawaki Mai Tuta, Aminu Babba Da-Agundi da tsohon Ciroman Kano, Sunusi Ado Bayero majalisar masarautar.

A ranar Litinin Sarkin ya sanar da nade-naden a cikin wasikar da Masarautar Kano ta aike zuwa Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, dauke da sa hannun Dan Rimin Kano Alhaji Sarki Waziri, don neman sahalewar gwamnatin jihar.

Idan za a iya tunawa a shekarar 2003 ne Masarautar Kano, karkashin marigayi Alhaji Ado Bayero, mahaifin Sarki Aminu ta sauke Aminu Babba Dan-Agundi daga kujerarsa saboda rashin ladabi.

Daga baya Kotun Koli ta tabbatar da cirewar da Sarki Ado Bayero ya yi wa Aminu Babba Dan-Agundi.

Kazalika, a shekarar 2014 tsohon sarki Muhammadu Sanusi II ya cire Sanusi Bayero daga matsayinsa na Ciroman Kano saboda kin yi masa mubayi’a.

To sai dai a wani mataki mai kama da mi’ara koma baya ga hukuncin mahaifinsa, Sarki Aminu Bayero ya mayar da mutanen biyu matsayinsu tare da kara musu daraja.

Yanzu Dan-Agundin shi ne Sarkin Dawaki Babba, shi kuma Sunusi Bayero ya zama Wamban Kano.

‘Matakin ci baya ne ga masarutun gargajiya’

To sai dai a nasa tsokacin, Babban Darektan kungiyar rajin tabbatar da adalci da daidaito (CAJA) Kabiru Dakata, ya ce yanzu ta bayyana karara cewa ba sarki ke jagorantar masarauta ba, gwamnan da ya nada shi a kan kujerar ne ke jan akalarsa domin biyan bukatunsa na siyasa.

Da yake jawabi a madadin gamayyar wasu kungiyoyi sama da 50 masu rajin kare mutuncin Kano, Kabiru Dakata ya ce wannan dalilin ne ya sa aka yi ta sa-toka-sa-katsi tsakanin gwamnan da tsohon sarki Muhammadu Sanusi II.

Ya ce, “A baya sai da Gwamna Ganduje ya nemi Sarki Sanusi ya dawo da Dan-Agundin kan kujerarsa amma sarkin ya ki bisa hujjar cewa hakan tamkar cin mutunci ne ga masarautar da tun da farko ta dakatar da shi saboda rashin biyayya.

“Shi kuma sarkin ya ki yarda yana mai cewa ba zai yi karan tsaye ga batun da yake gaban kotu ba.

“Wannan babban ci baya ba ne ga harkar sarauta, ko da yake ba mu yi mamaki ba.

“Kowa ya san Babba Dan-Agundi aminin Ganduje ne a siyasance, ka ga ke nan dole yanzu zai cika masarautar da ‘yan hannun damanasa.

“Idan har da gaske masarautar ta yi domin gyara dangantaka tsakanin iyalan gidan Bayero da gidan Dan-Agundin, me ya sa ya hana a dauko wani mutum daban daga gidan Dan-Agundi a ba shi sarautar, sai ka je ka dauko wanda ya ci mutuncin mahaifinka?

“Abun da sabon sarkin ke nunawa duniya karara shi ne ya fi mahaifinsa sanin abun da ya kamata”, inji shi.

Karan tsaye ne ga doka –Farfesa Yahaya

Shi ma a nasa tsokacin, fitaccen masanin tarihi a Kano, Farfesa Dahiru Yahaya ya ce matakain shi ne kololuwar karan tsaye ga doka da kuma masarautun gargajiya.

Ya ce, “La’akari da hukuncin Kotun Koli, marigayi Ado Bayero ya yi daidai ke nan kan cire Dan-Agundi. Hakan ya nuna Dan-Agundin ya karya doka, to a kan wane dalili za a sake nada wanda ya karya doka?

“Abun da nake cewa shi ne bai kamata ba a nada mutumin da kotu ta tabbatar mai laifi ne, ko da kuwa a wani mukamin ne ba wannan ba, kuskure ne kuma abin kunya ne.

“Me su ke so su mayar da sarautun gargajiyarmu ne?

“Wannan abin kunya ne ko da kuwa Sarkin Dawakin Duniya suke so su mayar da shi”, inji Farfesa.

‘Ganduje ba zai yi abun da ya saba wa doka ba’

Shi kuwa a nasa bangaren, babban hadimin Gwamana Abdullahi Ganduje kan Masarautun Gargajiya, Alhaji Tijjani Mailafiya Sanka ya ce gwamnan ba zai yi abun da ya saba wa doka ba.

“Na yi amanna Masarauta ba za ta yanke wata shawara ba tare da tuntubar masana shari’a ba ko harkar tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

“Maganar Sarkin Dawaki Mai Tuta tuni ta riga ta zama tarihi tun lokacin da Kotun Koli ta yanke hukunci a kai, kuma tuni ya rungumi hukuncin tare da addu’ar Allah Ya musanya masa da mafi alheri, wata kila Allah ne Ya amsa addu’ar tasa”, inji Mailafiya Sanka.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton Dan-Agundi bai ce uffan ba a kan lamarin.