✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nada magoya bayan Al-Bashir a mulkin Sudan na ta da kura

Sama da mutum 100 ne aka kashe a watan Oktoban bara.

A yanzu shekara uku ke nan da kifar da gwamnatin tsohon Shugaban Sudan Janar Omar Hassan Al-Bashir bayan wata zazzafar zanga-zanga.

An gano cewa sojoji na bai wa ’ya’yan jam’iyyarsa ta National Congress Party (NCP) manyan mukamai, wanda hakan ya sa ake fargabar za su iya dawowa da karfinsu a fagen siyasa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Gwamnatin hadaka da aka kafa ta zo karshe a bara, bayan Janar Abdel-Fattah Burhan ya yi juyin mulki ga fararen hular da suka taka muhimmiyar rawa a gagarumin boren da ya kawo karshen mulkin Al-Bashir.

Sai dai a yanzu da dama na ganin cewa sojoji da sauran mambobin Majalisar Tsaro na goyon bayan tsofaffin jami’an gwamnatin, wadda ta gudanar da Shari’ar Musulunci mai tsauri a lokacinta.

Hamza Balol, wanda jigo ne a Kungiyar Rajin Demokuradiyya ta FCC da aka kafa gwamnatin hadin-gwiwa tare da sojoji, na ganin cewa sojojin sun yi wa tafiyar zamba cikin aminci.

A cewarsa wadanda suka yi juyin mulkin “Na bai wa shugabannin tsohuwar gwamnati dama don su samu shiga a fagen siyasa.

“Dole ne kungiyoyin farar hula su hada hannu su kawo karshen wannan juyin mulki,” inji Mista Balol.

Sama da mutum 100 ne aka kashe a watan Oktoban bara, a jerin boren da aka rika gudanarwa na bukatar a mayar da kasar ga mulkin farar hula.

Daya daga cikin umarnin da Janar Burhan ya bayar bayan juyin mulkin shi ne na dakatar da ayyukan kwamitin da aka kafa don lalubo hanyoyin ci gaba bayan kifar da gwamnati, sannan ya soke dukkan matakan da kwamitin ya dauka.

Kwamitin a karkashin wani lauya, mai suna Wajdi Saleh da aka tsare bayan sojoji sun kwace mulki, ya yi kokari wajen bankado cin-hanci da rashawa da ake zargin ya zama ruwan dare a zamanin Al-Bashir.

Ya bankado sunayen jami’an ’Yan sanda na ba da kariya wajen rusa gidan Musulmin da suka yi zanga-zanga kan bataci ga Annabi a Indiya, gwamnati da ’yan kasuwa, tare da kwace kadarori da rufe asusun ajiyar mutane da dama.

Haka ma kwamitin na bincike kan huldodin da suka gudana a tsakanin shugabannin NCP da manyan Janar-Janar bayan an yi juyin mulki.

Sai dai kwamitin ya fuskanci suka daga wadansu da suke ganin yana aiki ne ba bisa ka’ida ba, kazalika ya zama wani makami na muzguna wa wadansu.

Bayan juyin mulkin, an yi zargin sojoji sun yi kokarin kulla huldar kut-da-kut da Jam’iyyar NCP da ’yan korenta, don su samu damar dorewa a kan mulki.

Daruruwan ma’aikata da aka kora a Babban Bankin Kasar sun dawo aiki, haka a Ma’aikatar Shari’a da kafafen yada labarai da sauran ma’aikatun gwamnati.

Daga cikinsu akwai Janar Ahmed Mufdal, tsohon Gwamnan Kudancin Kordofan kuma tsohon Shugaban NCP.

A yanzu shi ne Shugaban Sabuwar Hukumar Samar da Bayanan Sirri da aka yi wa garambawul, wadda a lokacin mulkin Al-Bashir ta zama tamkar dodo.

An kuma saki wadansu daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar NCP da ake tsare da su, tare da bude musu asusan bankinsu.

Yanzu haka tsohon Shugaba Al-Bashir na tsare a hannun sojoji bayan kama shi da zargin cin- hanci da rashawa a shekarar 2019.

Kuma tun a watan Yulin 2020 ake yi masa shari’a a kan juyin mulkin da ya yi, da ya kawo shi kan madafun iko a 1989.

Dama abin da masu rajin kare demokuradiyya ke fatan gani ke nan, kuma an fara shari’ar ce tun kafin Janar Burhan ya ƙwace mulki. A yanzu sojojin sun ki mika Bashir ga Kotun Duniya mai hukunta manyan laifuffuka don fuskantar tuhuma kan rikicin Dafur, zargin da ya musanta.

Wadansu masu sharhi sun yi amanna cewa a karshe sojojin za su saki tsohon Shugaban, kamar yadda aka saki Shugaba Hosni Mubarak a Masar bayan sojoji sun kwace mulki a shekarar 2013.

Ali Karti wanda shi ne Shugaban Riko na Kungiyar Musulunci ta Sudan (Sudan Islamic Mobement), wata hadakar kungiyoyin Musulunci, shi ne ake ganin kashin bayan dawowar Jam’iyyar NCP.

Yanzu haka yana zaune ne a Turkiyya, kuma ya yi hira ta talabijin a karon farko cikin sama da shekara uku.

A hirar ya kare NCP, ya kuma ce jam’iyyun Musulunci na bukatar kwaskwarima don shiga zabe mai zuwa.

Mista Karti wanda tsohon Ministan Harkokin Wajen Sudan ne na cikin jerin mutanen da kwamitin da ke aikin bankado badakalar da aka yi a gwamnatin Bashir ke nema.

An kwace daruruwan filayensa da ke Arewacin Khartoum, kuma ya musanta aikata ba daidai ba.

Ana kuma zarginsa da hannu a muzguna wa masu neman ’yancin kafa kasar Sudan ta Kudu a karkashin rundunar soji ta Popular Defence Forces da aka kafa a shekarun 1990.

Shi ma tsohon Ministan Yada Labarai na Sudan, Amin Hassan Umar wanda aka yi hira da shi a baya-bayan nan ya nanata cewa akwai rundunar Musulunci mai mayaka 500,000 da ke shirye su kare Sudan daga barazana.

Duk da ba za a iya tantance gaskiyar ikirarin nasa ba, idan har gaskiya ne, akwai adadin wadannan mayaka 500,000, to kuma sun fi karfin rundunar Rapid Support Forces (RSF), wadda ta kunshi mayakan Janjaweed da ake zargi da aikata miyagun laifuffuka a yakin Dafur.

An kiyasta cewa RSF na da mayaka daga 50,000 zuwa 150,000.

Wadansu masu sharhi sun yi amanna cewa manyan sojoji da suka hada da Janar Burhan na amfani da kungiyoyin Musulunci don rage karfin fada-a-ji da Kwamnadan RSF Janar Muhammad Hamdan Dagalo ke da shi.

Yanzu haka Janar Dagalo ne Mataimakin Shugaban Sojojin da suka yi juyin mulki a Sudan.