✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nadin sababbin ministoci: Kar dai a kuma

Sai bayan watanni talatin da daya ne aka yi wa wasu jiga-jigan ’ya’yan jam’iyyar APC da suka taru suka cicciba Shugaba Muhmmadu Buhari bisa mulki…

Sai bayan watanni talatin da daya ne aka yi wa wasu jiga-jigan ’ya’yan jam’iyyar APC da suka taru suka cicciba Shugaba Muhmmadu Buhari bisa mulki sakayya, alhali kuwa zufar gaban goshinsu ta dade da bushewa, da yawa kuma sun dade da  komawa ga Mahakicinsu game da haka bayan sun yi ta zaman tammahan-wa-Rabbuka game da haka. To, kwatsam a daidai karshen watan jiya sai ga shi gwamnatin Shugaba Muhammadu Bauhari ta fitar da mukaman da aka rigaya aka kagara ta firfitar na mutanen da aka zazzabo don doddorawa bisa shugabancin hukumomi da  ma’aikatun gwamnatin tarayya, su kusan dubu biyu.

To, amma maimakon haka ya dadada ran jama’a sai ma cewa suke yi abin haushi ya ba su, domin kuwa ya zo ne a ba-zata, jerin sunayen ya kunshi wadanda ba ‘yan siyasa ne ba, sai dai wadanda aka yi wa alfarma da kuma na wasu  cima-zaune. Haka nan kuma jerin sunayen ya tayar da kura ainun sa’ilin da aka tsintsinci sunayen wasu matattu a ciki aka kuma yi sakacin kawar da su,  har sai da hakan ya nuna rashin dacewarsa don kin bibiyar ainihin abin da ya kunsa kafin a sanarwa jama’a. 

To, tun kafin a kai ga haka, a watan Oktobar shekarar da ta gabata Shugaba Buhari ya ce ba ma nannada wasu zaratan ‘ya’yan jam’iyyar zai yi bisa wadancan mukaman ba, har ma kara yawan ministocinsa zai yi, domin kuwa ya fahimci cewa a yanzu akwai matukar bukatar fadada Majalisar Zartarwa ta Tarayya.  To shi ne jama’a ke fatan cewa kada dai a koma gidan jiya, watau yadda aka yi wadancan mukaman da aka nada a makon jiya ba su burge jama’a  ba.

Da farko dai Shugaba Buhari ya ce ba zai nannada ministoci da yawa ba saboda yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, amma zai zazzabo dai-dai daga kowace jiha don bin ka’idar da ke kunshe cikin kundin tsarin mulki da ya bukaci  akalla kowace jiha ta samu minista. Shi ya sa da ya tashi zubin ministocin, tun da farkon hawansa mulki, sai ya buge da cike guraben guda talatin da shida maimakon guda arba’in da biyu da gwamnatin jam’iyyar PDP ta bar masa.  Wannan ne ya sa shi rage yawan ma’aikatun da ya gada  ta hanyar hade wasunsu  wuri guda. Daga cikin  ministocin da ya nada  akwai guda goma sha hudu a matsayin kananan ministoci da kuma manyan ministoci guda ashirin da biyu, ciki har da shi kansa.

To yanzu  Shugaba Buhari ya ce tun da yake tattalin arzikin kasa ya ingantu za a koma bisa wancan tafarkin ta ministoci arba’in da biyu, watau za a yi karin wasu  guda shida ke nan. An fahimci cewa Shugaba Buhari na da nufin tsattsaga wasu manyan ma’aikatun da ake da su ne a halin yanzu, kamar  ma’aikatar Wutar Lantarki da Ayyuka da Gidaje, ta yadda ko wanne bangare daga cikinsu zai yi zaman kansa. Haka nan kuma za a raba ma’aikatar sufuri gida biyu: a samu ta sufurin jiragen kasa da kuma ta jiragen sama. Ita ma ma’aikatar aikin gona, daya daga cikin manyan ma’aikatun da ake da su, za a raba ta biyu don a fitar da Ma’aikatar Noman Rani Da Ban Ruwa.

Kamar yadda ake rade-radi, za a kuma yi garambawul a Majalisar Zartarwa ta Ministoci, inda ake cewa za a zazzare wasu guda takwas wadanda za a maye gurabansu da wasu sabbin jini don a ji dadin gungura gwamnatin yadda ya kamata. Haka nan kuma sauran tsoffin ministocin, da ba a tankade ko aka rairaye ba, za  a cancanja masu ma’aikatun da za su dudduba. Wannan al’amari ne da ya kamata a ce an yi tun a shekarar da ta gabata, yayin da talakawa suka fara kosawa da gwamnatin, ganin yadda take jan-kafa da kuma yadda  al’amuranta ba su gudana yadda ya kamata. 

To, sa’ilin da talakawa ke murna cewa an dauki matakan zaburar da gwamnati don yin ayyukan da za su fitar da jama’a daga kangin fatara da talauci, ko kuma a ce halin kunci da matsi, sai ga shi nan kuma murnarsu na so ta koma ciki, domin kuwa Shugaba Buhari ya  danka wannan muhimmin batu ga jam’iyyarsa da kuma gwamnonin jihohi wadanda yake gani su ne za su zazzabo masa wadanda suka fi dacewa ya tafi tare da su. Talakawa na ganin cewa da sake, ko kuma akwai gyara game da haka, domin kuwa  jam’iyyar APC dai a halin yanzu tana fama da matsaloli masu yawan gaske wadanda suka kusan kai ta kasa, saboda haka nan idan har tana cikin masu zakulo wadanda Shugaba Buhari zai nannada ministoci, to kunshi za a yi a baraka, watau za a yi ne ba a yi ba, domin zaben tumun dare kawai za a yi. Dalili kuwa shi ne  ganin  cewa bakin shugabannin jam’iyyar daya ne da na gwamnonin da ba su tare da sauran ’ya’yan jam’iyya.

Saboda haka maimakon daure kashi igiya kawai za a bata, kuma hakan ba zai taimaka  wajen dinke barakar da ta gauraye jihohi kusan goma sha shida da jam’iyyar APC ke mulki ba. 

To, amma ana iya cewa Shugaba Buhari ya nemi gwamnoni da uwar jam’iyya ne su taimaka masa dangane da haka don ya kore ya sha da karari idan aka zo babban taron jam’iyyar na kasa baki daya, wanda a lokacin ne za a fitar da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, inda yake sa ran cewa gwamnoni da shugabannin jam’iyyar za su rama wa kura aniyarta, za su saka  masa da kuri’un wadanda ake kira delegates daga jihohinsu. To koma dai mene ne dalilin Shugaba Buhari na amincewa da gwamnoni da kuma uwar jam’iyya game da haka ana iya cewa wanda ya sanya takalmi shi ya fi sanin inda ya matse shi. 

Ya kamata fa a tuna cewa mutanen da gwamnonin nan za su zazzakulo, su tura wa Shugaba Buhari, suna iya kasancewa ba su ne wadanda  jama’ar jihohinsu ke bukata ba, kuma wajibi ne a yi la’akari da cewa yawancin gwamnonin nan ba su danyen ganye  da ’yan Majalisar Dattijai daga jihohinsu, wadanda kuma ta kansu za a bi kafin a tantance sababbin ministocin da za a nannada. Ashe ke nan ya wajaba a yi taka-tsantsan game da haka, ganin cewa har yanzu ana takun saka tsakanin Majalisar Dattijai da kuma bangren gwamnati, kuma batun tantance sababbin ministocin kan iya janyo sabon jidali a tsakaninsu, domin dattijan za su nuna amincewa ko akasin haka ga wadanda aka zazzabo daga jihohinsu, tun da dai mafiya rinjaye daga cikinsu ’ya’yan jam’iyyar APC ne.

A karon farko dai an ce Shugaba Buhari da kansa ne ya zazzabo ministocin da yake aiki da su a yanzu, kuma tun kafin a tafi ko’ina sai aka fara kuka da su, saboda abin da ake cewa rashin sanin makamar aiki, domin da yawansu ba ’yan siyasa ba ne.  To, a wannan karon ya kamata Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa wadanda za a kawo masa ya yi aiki da su kwararru ne, kuma  zakakuran hazikan da suka yi fice a harkokin siyasa da mulki, ba bara-gurbin  da gwamnoni za su turo masa  daga jihohi ba, wadanda  cikin dan kankanen lokaci za su farfashe, su cika wuri da doyi.