✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC ta kama dan kasuwa da maganin Maleriya na jabu a Onitsha

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) ta kama wani mai suna dan kasuwa, Obinna Igbo, bisa zargin shigo da maganin Maleriya…

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) ta kama wani mai suna dan kasuwa, Obinna Igbo, bisa zargin shigo da maganin Maleriya samfurin Amnata na jabu.

An dai bayyana kamo wanda ake zargin wanda dan kasuwa ne mai shekaru 32 a wata sanarwa da kakakin hukumar, Mista Olusaye Akintola ya fitar ranar Litinin.

Akintola ya ce wanda ake zargin da ya shiga da magugunan da ba a yi wa rijista ba, kuma an gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, wacce alkali Tijjani Ringim ke jagoranta.

Ana dai tuhumarsa da laifuka hudu da suka hada da shigo da kaya ta haramtacciyar hanya, mallaka da siyarwa, da rarraba magungunan jabu da suka hada da Amnata Forte mai nauyin miligram 89, da kafso din Lumefantrine mai nauyin miligram 480 a kasuwar Onitsha da ke Jihar Anambra.

Kazakika, shagungunan da aka kama wanda ake zargin na sayar da magungunar bayan shigo da su sun hada da shago na 200, Da Freedom Line, da kuma babbar kasuwar Onitsha.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa Babbar Daraktar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce wadanda ake zargin sun shiga hannun hukuma ne yayin binciken sashin bincika da tabbatar da doka na hukumar.

Ta kuma ce yanzu haka an rufe uku daga cikin shagunan da hukumar ta gano Mista Igbo ya siyar wa da maganin, har sai ta kammala bincike.

Da take binciken shugabannin shagunan kan siyar da jabun magunguna, hukumar ta NAFDAC ta gano cewa su ma sun siyo shi ne daga Babban Daraktan katafaren shagon magani na OJ Don Global wanda mallakin Igbo ne.

Da fari da hukumar ta gaza kamo Igbo domin samu labarin hukumar ta baza komarta domin kamo shi ya sanya ya tsere, sai dai daga baya ta kamo shi a Onitsha, ta hanyar amfani da na’u’rar bibiya.