✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAFDAC ta kwace jabun magunguna na N20m a kasuwar Zariya

Magungunan sun hada da wadanda aka tanadar don raba wa ‘yan gudun hijira kyauta a jihar da wadanda akan bai wa mata masu nakuda da…

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta kama tare da kwace jabun magunguna na kusan Naira miliyan 20 a Jihar Kaduna.

Kamen wanda hukumar ta yi a ranar Litinin, ya hada ne da magungunan da ba su da rajista da kuma wadanda wa’adin aikinsu ya kare.

NAFDAC ta kwace magungunan ne a tsakanin shaguna 26 da ke Kasuwar Sabon Gari cikin Karamar Hukumar Zariya da ke jihar.

Magungunan sun hada da wadanda aka tanadar don raba wa ‘yan gudun hijira kyauta a jihar da wadanda akan bai wa mata masu nakuda da sauransu.

Hukumar ta ce da damar maganin ya lalace ne saboda rashin samun ajiyar da ta dace.

Da yake yi wa manema karin haske, Mataimakin Darakta na Sashen Bincike na NAFDAC reshen jihar ta Kaduna, Tamanuwa Andrew, ya ce, wannan bangare ne na kokarin da hukumar ke yi wajen yaki da jabun magaunguna a kasar nan.

(NAN)