✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC ta rufe kamfanin madarar yogot 4 a Kaduna

Kamfanonin na aiki ba bisa ka'ida ba a Jihar Kaduna.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta rufe masana’antun madarar yogot guda hudu a Kaduna. 

Shugaban Ofishin NAFDAC na Jihar Kaduna, Nasiru Mato, ya sanar da manema labarai a ranar Juma’a, 8 ga watan Oktoba, 2021 cewan an rufe kamfanonin ne saboda ba su da lasisi.

Ya  ce: “Ruwa da dukkannin abubuwan da ake sarrafawa da madara suna da matukar muhimmanci a ba su kulawa ta musamman don kare al’umma daga cin gurbatattun abubuwa”.

An gano kamfanonin madarar ne a lokacin da jami’an NAFDAC suke zagayen duba tsafta da ingancin abubuwan da kamfanoni ke sarrafawa, don tabbatar kare lafiyar masu amfani da su.

Nasiru Mato ya kara da cewa wannan ne ya sa NAFDAC ke kara sanar da al’umma cewa ya zama wajibi ga duk masu sarrafa irin wadannan abubuwa da su tabbatar sun bi kai’dojin da hukumar ta sa don kauce wa matsalar da za ta iya haifarwa.

Daga karshe ya ce za su cigaba da bincike a dukkanin lungu da sakon jihar.