✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC ta yi gargadi kan bullar rigakafin COVID-19 na bogi

Shugabar ta ce hukumar za ta ci gaba da sa ido a kan irin wadannan kayayyakin ba dare ba rana domin tabbatar da ingancinsu a…

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gargadi ’yan Najeriya kan yuwuwar bullar wasu alluran rigakafin COVID-19 na jabu a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da yaki da cutar.

Babbar Daraktan hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye wacce ta yi kiran ranar Alhamis a Kano yayin bikin lalata jabun magunguna da wadanda suka gama aiki na shiyyar Arewa Maso Yamma na kusa Naira miliyan 613.3 ta kuma ce dole mutane su yi taka-tsan-tsan.

Shugabar ta ce hukumar za ta ci gaba da sa ido a kan irin wadannan kayayyakin ba dare ba rana domin tabbatar da ingancinsu a Najeriya.

Farfesa Mojisola, wacce Darakta a sashen bincike na hukumar, Barista Kingsley Ejiofor ya wakilta ta kuma ce, “Yin jabun magunguna wani salo ne na yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wanda kuma babbar barazana ne ga lafiyar al’umma.

“NAFDAC za ta ci gaba da tabbatar da cewa magungunan da abincin da ake sarrafawa, rarrabawa da kuma sayarwa a Najeriya masu inganci ne.”

Kayan da aka lalata dai yayin bikin sun hada kwayoyi, magungunan hawan jin da na zazzabin cizon sauro, magungunan kara kuzari, kayan abinci irinsu taliya, man girki, lemukan kwalba, mayukan shafawa da dai sauransu.