✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naira biliyan 305 muke bukata don gudanar da zaben 2023 —INEC

Naira biliyan 189 INEC ta kashe wajen gudanar da babban zaben kasa a shekarar 2019.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bukaci Naira biliyan 305 a matsayin kudin da zai wadata ta gudanar da babban zaben kasa a shekarar 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa a ranar Litinin.

Bayanai sun ce Farfesa Yakubu wanda ya amsa goron gayyatar Majalisar, ya gabatar da kasafin kudaden da Hukumar INEC za ta kashe wajen gudanar da zaben 2023 a cikin kasafin kudadenta na 2022.

Ya ce kasafin Naira biliyan 140 da aka yi wa INEC tanadi domin gudanar da harkokinta na badi, daga ciki Naira biliyan 40 ne kasafinta kamar yadda aka saba, yayin da kuma Naira biliyan 100 ake sa ran ta fara shirye-shiryen gudanar da zaben na 2023.

Sai dai ya ce Naira biliyan 100 din da aka ware a cikin kasafin ba zai wadatar ba wajen gudanar da zaben na 2023, lamarin da ya ce akwai bukatar karin Naira biliyan 205.

Da yake kare kasafin, Farfesa Yakubu ya ce INEC tana da zabukan cike gurbi guda takwas da za ta gudanar a badi da suka hada da na ’yan Majalisar Tarayya uku da na ’yan Majalisar Dokoki a jihohi biyar gami da kuma zaben gwamna a jihohin Ekiti da Osun.

Kazalika, ya ce akwai wasu shirye-shirye da hukumar ke bukatar ta kammala gabanin zaben ya wakana, inda ya bayar da misalin wasu muhimman kayayyakin zaben da za a tanada kamar akwatin zabe, buga takardu masu dauke da sunayen masu ’yan takara da kuma katin zabe da sauransu.

Naira biliyan 189 aka kashe a zaben 2019

Waiwayen da Aminiya ta yi ya gano cewa Naira biliyan 189 Hukumar INEC ta kashe wajen gudanar da babban zaben kasa a shekarar 2019.

Kididdiga masu lisaffi ya nuna cewa an kashe naira 2,249 kan kowace kuria guda da aka jefa a zaben na 2019.

Hakan dai yana kunshe cikin rahon zaben mai shafi 384 da Farfesa Yakubu ya fitar a watan Nuwambar 2020.

A shekarar 2018 ce Majalisar Dokokin Tarayya ta sahale wa INEC kashe Naira biliyan 189 a zaben na 2019 kamar yadda ta bukata.