✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naira ta shiga jerin kudaden da darajarsu ta fi faduwa a duniya

Yayin da darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kan kudaden waje, a yanzu dai kudin na Najeriya ya shiga sahun kudaden da darajarsu…

Yayin da darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kan kudaden waje, a yanzu dai kudin na Najeriya ya shiga sahun kudaden da darajarsu ta fi faduwa a fadin duniya a bana.

Darajar kudin na bin bayan kudin Sidi na Ghana a lalacewa, inji wani sabon rahoto da jaridar Bloomberg ta Birtaniya ta wallafa a ranar Litinin.

Rahoton ya ce, Naira a yanzu ta shiga sawun kudin Kasar Saliyo wanda ya fadi da kasa da kaso 36 cikin 100, da kudin Fam na Misira wanda ya fadi a daraja da kaso 35.

Sai kuma Sidi na Ghana wanda ya fadi a daraja da kashi 55, da kuma Rupee na Sri Lanka.

Bloomberg ta rawaito cewa kodayake Gwamnatin Najeriya ce ke kayyade darajar Nairar, amma a kasuwar bayan fage ne a ke sanin hakikanin darajar Naira daga yawan sayen Dalar da ake yi.

Talakawa da kananan ‘yan kasuwa ne za su fi jin radadin tashin gwauron zabin da Dala ta yi, inji sabon rahoton.

Canjin Dala da Naira a hukumance N442.75 ne a ranar Juma’a, amma masu sayar da Dalar a kasuwar bayan fage a sai da suka kai ta N890.

Faduwar darajar Naira ita kadai ta taimaka wajen sa farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya, ga kuma bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara da ke tafe.