✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naja’atu Muhammad ta bayyana dalilin ficewa daga APC

Dole na fito a yi gwagwarmaya da ni wajen ceto Najeriya daga halin da take ciki.

Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta fice daga jam’iyyar APC mai mulki a kasar yayin da Babban Zabe ya karato.

Hajiya Naja’atu ta sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 19 ga Janairun 2023, wadda ta aike wa Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Naja’atu wadda yanzu haka Kwamishina ce a Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda a Najeriya, ta ce kalubalen da kasar nan ke fuskanta a yanzu ya sanya dole ta fito daga takunkumin duk wata jam’iyya don ta shiga gwagwarmayar kai kasar nan zuwa tudun tsira.

A wata sanarwa da fitar a wannan Asabar din, Naja’atu ta ce duk jam’iyyyu a fadin kasar nan ba su da wani bambancin akida.

Ta bayyana ta cewa jam’iyyun kasar kamar tufafi mabanbanta da ’yan siyasa sukan saka don wata bukata ta kansu kebantacciya.

’Yar siyasar ta ce ta mayar da hankali wurin goyon bayan jama’a da ke da burin shawo kan matsalar kasar nan tun daga tushe a Najeriya.

“Watsi da siyasar jam’iyyu a wannan lokacin yana daya daga cikin wadannan matakan.

“Kowa ya san cewa Najeriya tana fuskantar kalubale daban-daban da suka hada da rashin tsaro, talauci, rashin daidaito da rashin samun ababen more rayuwa.

“Wadannan kalubalen suna bukatar namijin kokari daga jajirtattun shugabanni masu kishin kasa a dukkan matakan gwamnati.

“Dole ne ’yan Najeriya sun san cewa akwai yiwuwar shiga matsanancin hali bayan sun kori shugabanni da suka gaza a kasar nan a cikin shekarun da suka wuce.

“Dole ne ’yan Najeriya sun san abinda hukuncinsu da zabinsu zai iya haifarawa. Don haka, ajiye zabin ka a jam’iyya daya na iya zama hatsari ga ci gaban kasar mu da dimokuradiyyarmu.

“A matsayina na ’yar Najeriya da ke da kishin kasa, a yanzu na mayar da hankali wurin gwagwarmayar tabbatar da adalci da kuma samar da daidaito a tsakanin al’umma.

“Ina da yakinin cewa duk ’yan Najeriya sun cancanci rayuwa mai aminci,”a cewar Naja’atu.