NAJERIYA A YAU: Dalilin Da INEC Ta Soke Rajistar Mutum Miliyan 1.2 | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Dalilin Da INEC Ta Soke Rajistar Mutum Miliyan 1.2

    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan.

Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) ta soke rajistar zaben ’yan Najeriya miliyan 1.126, wata biyar kafin babban zaben 2023.

Wadanda hukumar ta soke rajistar tasu sun kusa rabin mutum miliyan 2.5 da suka yi rajistar zabe daga watan Yunin 2021, zuwa 14 ga Janairu na 2022.

Me ya sa hukumar ta yi haka, ina makomar wadanda aka soke wa rajista, kuma wane tasiri matakin na INEC zai yi a zaben 2023?

Ku biyo mu cikin shirin domin jin amsoshin wadannan tambayoyin da ma wadansu karin bayanan.