✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani

Shin me ya sa wahalar man ta ki karewa duk kuwa da cewa an shawo kan mastalolin da aka dora wa laifin a baya?

More Podcasts

Domin saukewa latsa nan

Rige-rige da dogayen layikan ababen hawa sun ki karewa a gidajen mai sakamakon wahalar samun mai da ta ki ci, ta ki cinyewa a Najeriya.

A baya, rahotanni sun nuna danganta matsalar da gurbataccen man da aka shigo da shi da kuma rashin hanya saboda ambaliyar ruwa, da dai sauransu.

Shin me ya sa wahalar man ta ki karewa duk kuwa da cewa an shawo kan wadancan mastalolin da aka dora wa laifin a baya?

Shirin Najeriya A Yau, ya tattauna da masu ruwa da tsaki da masana kan al’amarin da kuma mafita.