NAJERIYA A YAU: APC A Idon ’Yan Najeriya Bayan Ta Tara Fiye Da N20bn | Aminiya

NAJERIYA A YAU: APC A Idon ’Yan Najeriya Bayan Ta Tara Fiye Da N20bn

Jam’iyyar APC
Jam’iyyar APC
    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Tun bayan bayyana kudin fom din takarar jam’iyyar APC ’yan Najeriya suke zura ido domin ganin wadanda za su saya.

Rahotanni sun bayyana cewa kudaden da jam’iyyar ta tara kawo yanzu, sun sa yawancin ’yan Najeriya sun saki baki saboda mamaki, lura da yadda APC din take yawan ambatar yaki da cin hanci.

’Yan Najeriya da masu sharhi sun bayyana wa shirin Najeriya A Yau  irin kallon da suke yi wa jam’iyyar, da kuma makomar matakin jam’iyyar na sayar da fom din takararta a kan farashin da ya zarce na sauran jam’iyyu.