NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Boko Haram Ke Yanka ’Yan Jari Bola A Maiduguri | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Boko Haram Ke Yanka ’Yan Jari Bola A Maiduguri

    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao

Domin sauke shirin latsa nan

A ’yan kwanakin nan rahotanni sun bayyana cewa ’yan Boko Haram sun yi wa ’yan jari bola sama da 50 yankan rago a kasa da wata guda a Jihar Borno.

Ko me ya janyo irin wannan hari ba kasafai ake samun irinsa ba?

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki daga Jihar Borno kan yadda abin ya faru, wadanda aka kashe da kuma dalilan maharan.