✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Hukuncin Dauri Kafin A Rataye Abdulmalik Bai Mana Ba —Dangin Hanifah

Dangin Hanifah, wadda malaminta, Abdulmalik Tanko, ya sace sannan ya kashe ta suna so a gaggauta aiwatar da hukuncin rataya da aka yanke mishi

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Iyayen karamar yarinyar nan Hanifa Abubakar, wadda malaminta ya sace sannan ya kashe ta a Kano, sun ce ba su gamsu da hukuncin daurin shekara biyar kafin a zartar mishi da hukuncin rataya ba.

A ranar 28 ga watan Yulin shekarar 2022 kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko da abokinsa wurin kisan Hanifa hukuncin dauri a gidan gyaran hali da kuma kisa ta hanyar rataya bayan sun cinye wa’adin da aka diba musu.

Wannan hukunci, da aka yanke bayan wata shida ana shari’ar kisan na ci gaba da samun sharhi daga bakin jama’a, ciki har da dangin Hanifa, wadda Abdulmalik Tanko ya halaka.

Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da kuma dangin marigayiya Hanifa kan wannan hukunci. A yi sauraro lafiya: