NAJERIYA A YAU: Shirin da matasan Najeriya ke yi wa zaben 2023 | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Shirin da matasan Najeriya ke yi wa zaben 2023

Wani mutum yayin da ya ke kada kuri’a a Zaben 2019
Wani mutum yayin da ya ke kada kuri’a a Zaben 2019
    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao da Bilkisu Ahmed da Isa Ismaila

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

A yayin da Zaben 2023 ke kara karatowa, hankalin duniya ya fara dawo wa Najeriya, lura da irin adadin ‘yan kasar da kuma zaman ta Giwar Afirka.

Masu hikima na cewa, matasa ne kashin bayan al’umma, shakka babu, ko wane irin tanadi matasan ke yi wa wannan zabe da zai bai wa sabbin shugabanni damar mulkarsu har na tsawon shekara hudu?

Wannan shi ne batun da shirin namu na wannan lokaci ya mayar da hankali akai.