✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya a Yau: Wane tsarin zabe ya fi dacewa a Najeriya?

Tsakanin ’yar tinke da zaben daliget wanne ne ya fi dacewa a Najeriya.

Domin sauke shirin, latsa nan

A yayin da matsaloli da zargin magudi ke ci gaba da mamaye zabukan  fitar da ’yan takara da na shugabannin jam’iyya da sauransu a Najeriya, wane tsarin zabe ne ya fi dacewa?

Majalisar Dokokin kasar na kokarin yi gyara dokar zabe ta yadda kowa zai samu shiga an dama da shi a zaben shugabanni; amma kuma ra’ayoyin ’yan Najeriya sun bambanta game da komawa amfani da tsarin ’yan tinke ko amfani da daliget.

Shirin Najeriya a Yau na wannan karon ya yi dubi ne a kan amfani da  tsarin ’yan tinke ko zaben daliget da kuma wanda a cikinsu kwalliya za ta biya kudin sabulu.

A yi sauraro lafiya.