Najeriya A Yau: Yadda bankuna ke ‘tatsar’ ’yan Najeriya | Aminiya

Najeriya A Yau: Yadda bankuna ke ‘tatsar’ ’yan Najeriya

Yadda bankuna suke zarar kudin caji daga asusun masu ajiya a cikinsu ya kai ’yan Najeriya makura.
Yadda bankuna suke zarar kudin caji daga asusun masu ajiya a cikinsu ya kai ’yan Najeriya makura.
    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Yawan tatsar ’yan Najeriya da bankuna ke yi ta hanyar cire-ciren kudi daga asusun masu ajiya ya kai ’yan kasar bango, tun suna gunaguni, har sun fara fitowa kafafen sada zumunta suna bayyana bacin ransu.

Me ya sa bankuna ke yawan zarar kudade ba tare da neman izini ba? Shin ’yan Najeriya na da damar bin kadun kudadensu a hukumance? Me doka ta ce a kan hakan?

Ku saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci, domin jin yadda aka yi aka haihu a ragaya.