NAJERIYA A YAU: Yadda daukar doka a hannu ke lakume rayuka a Najeriya | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Yadda daukar doka a hannu ke lakume rayuka a Najeriya

    Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Dabi’ar daukar doka da mutane ke yi a hannunsu ta hanyar kama mai laifi, sannan kafin a yi bincike su dauki hukunci ta hanyar duka, sara ko saka wa mutum taya a wuya a zuba fetur a cinna wuta, na dada karuwa a tsakanin mutane a ’yan kwanakin nan.

Rahotanni na yawan fitowa daga yankunan Kudu maso Yammaci da Arewa maso Yammacin Najeriya kan hukuncin na daukar doka a hannu.

Me yasa hakan ke yawan faruwa?

Ina mahukuntan kasar suke da har rai ke neman zama ba a bakin komai ba?