NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Kawar da ’Yan Fadar Buhari | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Kawar da ’Yan Fadar Buhari

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari
    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Shin akwai lokacin da zababbun shugabanni a Najeriya za su sauka daga kujerunsu idan suna son tsayawa takarar zabe?

Kawo yanzu dai, dokar zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a watan Fabrairu ta wajabta mishi sauke ’yan fadarsa masu niyyar shiga zabe.

Shin wane tasiri wannan sauyi da sabuwar dokar zai yi ga dimokuradiyyar kasar?

Wadannan da ma wasu batutuwan da suka shafi dokar zaben Najeriya ne batun da shirin namu ya mayar da hankali a kai. A yi sauraro lafiya.