NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget

Daliget a Jam’iyyun Siyasar Najeriya na shirin zaben fidda gwani
Daliget a Jam’iyyun Siyasar Najeriya na shirin zaben fidda gwani
    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

A ganinku daliget din jam’iyyu sun shirya yin abin kwarai a zaben fitar da ’yan takarar zaben 2023?

Kawo yanzu dai kasuwar daliget ce ke ci a siyasar Najeriya, saboda karatowar zabukan fitar da yan takara a jamiyyun siyasar kasar.

To sai dai kuma hankali ya koma kan gyaran da sabuwar dokar zabe ta yi kan wane ne daliget a zaben ’yan takarar da za su wakilci jam’iyyun siyasa a zaben 2023.

Muna tafe da karin bayani kan dokar da ta tantance wane ne daliget da kuma fashin bakin cukumurdar da ta dabaibaye zabukan fitar da ’yan takara domin zaben na 2023.