✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Yadda Sauyin Yanayi Zai Shafi Daminar Bana

Shawarwarin masana kan yadda za a takaita asarar amfanin gona

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Alamu sun fara nuna yadda sauyin yanayi zai shafi daminar bana, bayan hasashen hukumomin Najeriya suka yi kan ruwan sama da kuma katsewarsa a farkon daminar.

Ana ciki haka sai ga wata guguwa mai karfin gaske da ta shafi jihohin  Adamawa da Katsina a makon jiya.

Mun tattauna da Hukumar lura da yanayi ta Najeriya da kuma masanin kimiyyar noma domin jin yadda za a tunkari wadannan kalubalenen.