Najeriya A Yau: Yadda Tinubu da Dattawan Arewa Suka Yamutsa Hazo Kan Zaben 2023 | Aminiya

Najeriya A Yau: Yadda Tinubu da Dattawan Arewa Suka Yamutsa Hazo Kan Zaben 2023

    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao da Bilkisu Ahmed

Domin sauke shirin latsa nan

Bayyana aniyar takarar shugaban kasa a zaben 2023 da Bola Ahmed Tinubu ya yi a Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta tayar da kura a fagen siyasar Najeriya.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya zakulo dalilan Tinubu na bayyana maganar takarar tasa a Fadar Shugaban Kasa da kuma matsayar Kungiyar Dattawan Arewa dangane da wanda suke son ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023.