NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Ke Kallon Batun Tsige Buhari | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Ke Kallon Batun Tsige Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari
    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Tun ranar 28 ga Watan Yulin 2022 ne ’yan Majalisar Dattawan Najeriya na jam’iyyun adawa suka fara batun tsige Shugaba Muhammadu Buahri, kafin daga bisani takwarorinsu na Majalisar Wakilai su bi sahun su na ganin an tsige Buhari.

Maganar tsige Buhari na daga cikin batutuwan da ke cin kasuwarsu a tsakanin jama’ar kasar.

Shirin Najeriya A Yau ya binciko yadda batun ya samo asali da kuma halin da ake ciki zuwa yanzu.