NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Ke Rayuwa Cikin Kunci | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Ke Rayuwa Cikin Kunci

    Muhammad Auwal Suleiman da Bilkisu Ahmed

Domin sauke shirin latsa nan

’Yan Najeriya na kokawa bisa yadda rayuwa ke kara kuntata lokaci bayan lokaci, rana zafi, inuwa kuna, har wasu ma kan ce jiya ta fi yau, suna kuma tsoron zuwan gobe.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanan halin da ’yan Najeriya ke ciki na tsadar rayuwa da matsanancin raunin tattalin arziki; Mun kuma tuntubi masana kan abin da zai iya biyo baya in aka ci gaba da tafiya a haka.