NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Siyasa Ke Raba Kan ’Yan Najeriya, Su Kuma Kansu A Hade | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Siyasa Ke Raba Kan ’Yan Najeriya, Su Kuma Kansu A Hade

  Gangamin kamfe na Jam’iyyar APC
Gangamin kamfe na Jam’iyyar APC
    Bilkisu Ahmed da Halima Djimrao

Domin sauke shirin latsa nan

Najeriya kasa ce da Allah Ya yi wa dimbin arziki sosai.

Wasu na ganin a duk duniya babu kasa mai arziki kamar Najeriya, amma babu masu shan wahala kamar talawakawan kasar.

NAJERIYA A YAU: ‘Yadda na yi kundumbalar ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna’ -Tukur Mamu

Yadda ’yan Najeriya ke kokawa bayan litar fetur ta kai N600

Talakawan kasar na biye wa siyasa da ’yan siyasa, su yi ta ce-ce-ku-ce da fada da gaba, a wani lokacin ma har da kisan junansu a kan siyasa, a yayin da su kuma ’yan siyasar, manyansu da kananansu, kansu a hade kuma maganarsu daya.

Shirin Najeriya A Yau ya duba matsalar inda muka tattauna da wani dan siyasa da ’yan Najeriya da kuma masanin harkokin yau da kullum.