✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: ’Yan Najeriya Miliyan 19 Za Su Rasa Abinci —Rohoto

Zuwa watan Agusta yawan masu fama da yunwa a Najeriya zai karu da mutum miliyan biyar

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Wani bincike da cibiyar Cadre Harmonisé (CH) da ke bincike kan samuwar abinci a kasashen Yammacin Afirka da yankin Sahel ta gudanar tare da gwmantin Najeriya ya gano mutum miliyan 19.4 a kasar za su yi fama da yunwa a cikin ’yan watanni masu zuwa.

Rahoton ya nuna daga yanzu zuwa watan Agustan 2022, za a samu karin mutum miliyan biyar da ke fama da yunwa a jihohi 21 —kimanin mutum miliyan daya a duk wata ke nan.

Binciken da aka gudanar da hadin gwiwar Hukumar Noma da Samar Da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa a halin yanzu akwai mutum miliyan 14.4 da yunwa take addabar su a jihohi 21 a Najeriya.