✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA YAU: Za a koma biyan kudin haya wata-wata a Abuja

Tsakanin ’yan haya da masu gidajen haya wa zai fi amfana?

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Tsadar gidajen haya a Abuja ta sa yawancin mazauna birnin kan shafe shekara a koyaushe suna fadi-tashin tara abin da za su biya kudin haya.

Duk da haka, wasu masu gidaje a birnin ba sa karbar kudin haya sai na shekara biyu zuwa sama.

A kan haka ne Majalisar Dattawa ta fara aikin kafa dokar wajabta biyan kudin haya wata-wata a Abuja, maimakon shekara-shekara.

’Yan hayar Abuja sun bayyana wa shirin Najeriya A Yau yadda suke ji idan lokacinsu na biyan haya ya karato.

Akwai kuma bayanin abin da dokar ta kunsa, shin za ta yi aiki, kuma wa za ta amfana tsakanin ’yan haya da masu gidajen haya?