✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Da Bazar Wa Za A Yi Rawa A Sabuwar Tafiyar TNM?

Mene ne guzirin tafiyar TNM, ina aka dosa, kuma me za a ɗauko?

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Yayin da zabukan 2023 ke kara karatowa, fagen siyasar Najeriya sai kara tumbatsa yake yi.

Tuni ‘yan siyasa suka fara kai-kawo don fasalta bukatunsu da hanyoyin cimma buri.

A wannan yanayi ne wasu gaggawa ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso suka kudiri aniyar wata sabuwar tafiya.

Sai dai wasu na ganin ba a fage horar wannan tafiya a ka lokaci ba, yayin da wasu ke ganin don biyan boyayyiyar bukatar wani ko wasu za a yi ta

Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari a kan hakikanin inda aka dosa da guzirin da aka tanada da ma tsara bar da za a dawo da ita.