Najeriya A Yau: Yadda Rage Kwanakin Zuwa Makaranta Zai Shafi Dalibai A Kaduna | Aminiya

Najeriya A Yau: Yadda Rage Kwanakin Zuwa Makaranta Zai Shafi Dalibai A Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
    Bilkisu Ahmed and Mohammed Auwal Suleiman

Bayanin rage adadin kwanakin zuwa makaranta da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar a wannan zango ya dauki hankalin malaman makarantu da masana harkar ilimi a Jihar.

Malaman makaranta na ganin cewa tsarin da zai tilasta wa makarantu hutun kwana uku a sati  zai kara takure su wurin shirya jadawalin darussan da za su koyar.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da tattaunawa ta musamman da Malamai da masana harkokin ilimi akan wannan batu.