✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ba ta san da sayen makaman $875 daga Amurka ba —Minista

Gwamnatin Tarayya ta karyata labarin cinikin da ake cewa Majalisar Amurka ta hana.

Gwamantin Tarayya ta ce ba ta da masaniya game da batun sayo makamai na Dala miliyan 875 daga Amurka da Majalisar Dokokin Amurka ta hana a sayar wa Najeriya.

Ministsan Yada Labarai Lai Mohammed ya ce karya ce tsagoronta labarin da ya yi ta yawo game da sayo makaman da ake cewa Majalisar Dokokin Amurka ta hana a sayar wa Najeriya.

Lai Mohammed ya ce, “Babu wata yarjejeniyar sayen makamai tsakanin Najeriya da Amurka in banda na sayen jirage masu saukar ungulu kirar Super Tucano 12 wadanda shida daga cikin sun riga sun iso.”

Da yake sanar da cewa za a kaddamar jiragen guda shida da suka iso a ranar 3 ga watan Agusta, ministan ya ce Najeriya ta “Gamsu da dorewar hadin kan da muka samu daga gwamnatin Amurka a kan hakan.”

Ya kara da cewa, “Ba mu da wata masaniya game da kwangilar makamai ta Dala miliyan 875 ko helikwaftoci da ake cewa wasu ’yan Majalisar Amurka na kokarin shawo kan Shugaban Kasarsu kar ya girmama.

“Dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka tana da tafiya lafiya kalau kuma tana dada yin karfi,” inji shi.

Wasu rahotanni a makon nan sun bayyana cewa Kwamitin Harkokin Kasashen Wajen Amurka sun bukaci dakatar da sayar wa Najeriya wasu helikwaftocin yaki da kuma makamai kan zargin cin zarafin bil Adama a Najeriya.

Rahotannin sun ce kayan yakin da aka bayar da sautu sun hada da jirage masu saukar ungulu 12 AH-1 Cobra, injinan helikwaftoci 28 da kuma tsarin kula da zirga-zirgar jiragen soji guda 14. (NAN).